Gwamnan Kano Ya Karya Gwiwar Sheikh Daurawa, Ya Yi Murabus Daga Shugabancin Hisbah

Gwamnan Kano Ya Karya Gwiwar Sheikh Daurawa, Ya Yi Murabus Daga Shugabancin Hisbah

  • Daga karshe, shugaban hukumar Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi murabus daga kujerarsa ta shugabancin hukumar
  • Daurawa ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo daga jihar Kaduna inda ya ce ya yi mamakin maganganun da ya ji daga Kano
  • A baya, an yi ta yada jita-jitar cewa ya yi murabus inda malamin ya fito fili ya karyata labarin murabus din nasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Shugaban Hukumar Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi murabus daga kujerarsa a yau Juma'a 1 ga watan Maris.

Malamin ya tabbatar da murabus din nasa a cikin wani faifan bidiyo daya fito inda ya ke nuna rashin jin dadinsa kan abubuwan da suke faruwa.

Kara karanta wannan

Abin da Gwamna Abba ya fadawa malaman Kano da aka sa labule a fadar gwamnati

A karshe, Daurawa ya yi murabus daga kujerarsa kan wasu dalilai
Daurawa ya sanar da murabus daga Hisbah a Kano Hoto: Hisbah Command.
Asali: Facebook

Martanin Daurawa kan ayyukan hukumar

Shehin malamin ya ce ya yi iya bakin kokarinsa wurin kawo gyara don tsabtace harkar kafafen sadarwa da kuma fina-finai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya nemi gafarar Gwamna Abba Kabir ganin yadda ransa ya baci da kuma maganganu inda ya tabbatar da murabus daga kujerar.

Kano: Sheikh Daurawa ya ba Abba hakuri

"Ina daga nan jihar Kaduna yayin wani taro, sai naji wasu bayanai suna fitowa daga jihar Kano wanda sun kashe mani gwiwa.
"Abin da na ke ta kokari a Hisbah gyaran tarbiya kuma na yi iya yi na wurin zama da masu fina-finai da ba su shawarwari yadda za a gyara harkar fim.
"Haka na yi zama da 'yan TikTok wanda da kudin aljihunmu muka dauka muka ba su kudin mota tare da ba su shawarwari na addu'a."

- Aminu Ibrahim Daurawa

Kara karanta wannan

Akwai Matsala: Sai an gyara yadda Hukumar Hisbah take aiki a Kano inji Abba Gida Gida

"Amma duk da haka wasu ba su ji ba sun ci gaba bata tarbiya, amma ina bai wa mai girma gwamna hakuri saboda fushin da ya yi da maganganun da ya fada, ina rokon ya mani afuwa, na sauka daga wannan mukami."

- Aminu Ibrahim Daurawa

Gwamna Abba ya fusata kan ayyukan Hisbah

Kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya yi magana kan kura-kurai a yadda wasu hukumomi suke gudanar da aikinsu.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Abba Kabir ya koka kan yadda jami’ai kan ci zarafin wadanda ake zarfi da laifi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel