Kudin Tsafi: Yadda Wani Matashi Ya Yaudari ’Yan Mata 7 da Ya Hadu da Su a MyChat Ya Kashe Su
- Rundunar ƴan sanda a jihar Ogun ta samu nasarar cafke wani matashi mai suna Adebayo Olamide Azeez wanda ke kashe mata don tsafi
- Bayan da aka tuhumi Azeez, ya bayyana cewa daga watan Disamba 2023 zuwa kama shi ya kashe ƴan mata bakwai akan kuɗi naira 30,000
- Azeez ya sanar da cewa ya na haduwa da ƴan matan ne a wani dandalin soyayya na yanar gizo, inda ya ke kiran su zuwa gidansa a jihar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Ogun - A ranar Alhamis ne wani Adebayo Olamide Azeez ya bayyana yadda yake yaudarar matan wani dandalin soyayya "mychat" yana kashe su don yin tsafi.
An cafke Azeez ne bayan da aka yi zargin ya kashe wata mata Sulaimon Adijat, mai shekaru 35 don neman kudin tsafi.
Bayan kama Azeez, ya sanar da cewa ya shiga ƙungiyar ne a watan Satumbar shekarar da ta gabata kuma ya kashe mata bakwai, Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamishinan rundunar 'yan sandan jihar Ogun, Abiodun Alamutu ya ce wanda ake zargin ya hada baki da wani Moses Abidemi Awuraji, malamin tsubbu, wajen kashe matan don samun kudin tsafi.
Yadda nake yaudarar ƴan matan har na kashe su - Azeez
Da ya ke ba da labarin yadda ya ke yaudarar ƴan matan, Azeez ya ce:
"Ina haduwa da ƴan matan a dandalin yanar gizo na MyChat. Duk lokacin da Moses Awuraji ya ce yana bukatar jini, sai in shiga dandalin ina nemi mun hadu da wata.
"Nakan tattauna da duk wadda na gani a dandalin, in nemi mu hadu don mu yi lalata, mu yi cinikin kudin da zan biya ta da kuma inda za mu hadu. Mukan hadu ne a nan Atan-Ota."
Yadda Azeez ya ke kashe matan idan sun hadu
Ya ci gaba da cewa:
"Idan sun zo gida na, sai na dauke su na kai su gidan Moses Awuraji da ke a Igbo Olomi, Atan-Ota, sai mu kashe su a falon sa.
"Matar Abidemi (Awuraji Mariam) ce ke daure mun kafafuwansu ni kuma in shake masu wuya har su mutu."
Naira 30,000 zuwa naira 40,000 ake biyan Azeez
Tribune Online ta ruwaito Azeez na cewa bai da masaniyar yadda suke yi da gawar matan, amma dai ya ce ana biyansa naira 30,000 zuwa naira 40,000 idan ya kawo mace ya kashe ta.
"Ban san wanda suke sayarwa sassan jikin matan ba. Ni dai aiki na shi ne in nemo matan, in taimaka wajen kashe su, a biya ni kudi na in kama gaba ba."
A cewar Azeez.
Kwamishinan'yan sandan jihar Abiodun Alamutu, ya ce rundunar na aiki tukuru don gano matan da aka kashe tare da neman jama'a su shigar da rahoto idan ƴar uwarsu ta ɓata.
An kama kasurgumin mai garkuwa da mutane a Abuja
A wani labarin, rundunar ƴan sandan babban birnin tarayya ta ce ta cafke Abu Ibrahim, ƙasurgmin mai garkuwa da mutane da ya addabi garuruwan Abuja.
Rundunar ta ce ta kama mai garkuwan ne a wani sumame da ta kai dajin Sardauna da ke jihar Nasarawa, bayan samun sahihan bayanai.
Asali: Legit.ng