Kudin tsafi: Yadda wasu mutane 4 suka hallaka abokinsu suka guntule zuciyarsa

Kudin tsafi: Yadda wasu mutane 4 suka hallaka abokinsu suka guntule zuciyarsa

Wata babbar Kotun majistri dake garin Yaba na jihar Legas ta bada umarnin garkame wasu mutane hudu a Kurkukun IKoyi sakamakon kashe wani abokinsu da suka yi, sa’annna suka yanke zuciyarsa don yin amfani da ita wajen tsafe tsafe.

Mutanen sune Daniel Luka mai shekaru 24, Audu Isaiah, 24, Wavi David 20, da kuma Ayuba Musa 24, suna fuskantar tuhume tuhumen da suka hada da laifin kisan kai da kuma kulla mugun aiki.

KU KARANTA: Dakarun Sojin Najeriya sun yi ma masu garkuwa da mutane kisan kiyashi a Kaduna

Dansanda mai shigar da kara, Sajan Modupe Olaluwoye ya bayyana ma Kotun cewar matasan sun aikata laifin ne a ranar 22 ga watan Mayu a Ajah, wani gari dake gab da garin Legas, inda yace sun yi haka ne bisa umarnin wani Boka da ya bukacesu su kawo zuciyar mutum don su samu arziki.

Dansandan yace mutanen hudu sun ja abokin nasu mai suna James Isaiah mai shekaru 21 zuwa wani Daji, inda suka kashe shi ta hanyar amfani da wuka, suka kuma guntule zuciyar tasa, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Sai dai da yake dubunsu ta cika, Yansanda sun yi kokarin bin sawunsu har gida, inda suka daka musu wawa, a can suka kamesu gaba daya, sai dai har yanzu bokan da ya sanyasu wannan danyen aiki bai shiga hannu ba.

Jaridar The Nation ta ruwaito Dansandan ya nemi Alkalin Kotun ya yi duba ga sashi na 223, 233 da 165 na kundin hukunta manyan laifuka na jihar Legas don yanke musu hukuncin da ya dace dasu.

Sai dai dukkanin mutanen hudu sun musanta aikata laifin, don haka Mai sharia Oluwatoyin Oghere ya dage sauraron karar, kuma ya bada umarnin garkame su zuwa lokacin da babbab jami’I mai shigar da kara na jihar bada umarnin yadda za’a cigaba da shari’ar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel