Hukumar NCC Ta Umurci MTN, Glo da Sauransu da Su Toshe Layukan da Babu NIN, Ta Fadi Rana
- Hukumar NCC ta ba kamfanonin sadarwa izinin toshe layukan waya da ke aiki ba tare da an hada su da lambobin NIN ba
- Kamfanonin MTN, Airtel, Glo, 9mobile, da sauransu za su fara aiwatar da umurnin daga yau, Laraba, 28 ga watan Fabrairun 2024
- Layukan da abin zai shafa ba za su samu damar yin kira ko amsa kira ba, sannan ba za su iya aikawa sauran lambobi sakonni ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura
Hukumar Sadarwa a Najeriya (NCC) ta sake jadadda cewar wa'adin 28 ga watan Fabrairu da aka ba kamfanonin sadarwa don toshe layukan wadanda suka ki hada layukansu da NIN yana nan.
Aminu Maida, Mataimakin Shugaban Hukumar NCC, ne ya bayyana haka a wajen wani taro da aka gudanar a Kaduna ranar Laraba 28 ga Fabrairu, 2024.
NCC ta yi bayanin matakin na toshe layukan waya
Jaridar The Nation ta rahoto cewa Maida, wanda ya samu wakilcin Reuben Mouka, Daraktan kula da harkokin jama'a na hukumar NCC, ya jaddada muhimmancin wannan umurni.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa yana da matukar muhimmanci masu amfani da waya su bi ka’idojin da aka shimfida na hada NIN dinsu da layukansu don tabbatar da tsaron kasa baki daya.
Ya ce:
“Saboda haka, hukumar sadarwa ta kasa ta umurci duk kamfanonin sadarwa da su toshe layukan wayar mutanen da basu hada nasu da NIN ba a ranar ko kafin 28 ga watan Fabrairun 2024."
Ya kuma jaddada kudirin hukumar na kare hakkin jama'a da kuma bunkasar tattalin arziki, rahoton Punch.
Kotu ta hana kamfanonin sadarwa toshe layuka
A baya mun ji cewa an haramta wa Airtel, MTN da sauran kamfanonin sadarwa rufe duk wani layin waya wanda ba a hada shi da lambar shaidar dan kasa (NIN) ba.
Mai shari’a Ambrose Lewis-Allagoa na babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas ya ba da umarnin a ranar Litinin, 26 ga watan Fabrairu, inji rahoton Vanguard.
Hukuncin dai ya samo asali ne daga bukatar wani mai fafutukar kare hakkin bil adama, Olukoya Ogungbeje na neman dakatar da kamfanonin.
Asali: Legit.ng