Asiri Ya Tonu: Wani Magidanci Ya Halaka Ɗansa, An Gano Babban Dalili
- Jami'an 'yan sanda a jihar Abia sun kama wani tsoho mai shekaru 70, Marcel Udeh, kan zargin aikata kisan kai
- Ana zargin Udeh ya kashe 'dan cikinsa a yankin karamar hukumar Umunneochi saboda ya cinye abincin da ya rage masa a tukunya
- Kakakin 'yan sandan jihar Abia, Maureen Chinaka,ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce za a gurfanar da shi da zaran an kammala bincike
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura
Jihar Abia - Rahotanni sun kawo cewa wani mutumi mai suna Marcel Udeh, ya kashe 'dansa saboda abinci, a karamar hukumar Umunneochi ta jihar Abia.
Jaridar The Cable ta rahoto cewa Udeh, mai shekaru 70 wanda ya fito daga kauyen Eziama Lokpaukwu, ya gano cewa 'dansa ya cinye abincin karshe da ya rage masa a tukunya.
Cike da fusata, Udeh ya shiga cikin dakinsa sannan ya fito da bindiga ya harbe 'dan nasa, wanda hakan ne ya yi sanadiyar mutuwarsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Daily Post ta rahoto cewa, da faruwar lamarin sai mutanen garin suka kama Mista Marcel sannan suka daure masa hannayensa tare da daura shi kan gawar 'dan nasa.
Rundunar 'yan sanda ta yi martani
Da take martani kan lamarin, Maureen Chinaka, kakakin 'yan sandan jihar Abia, ta ce an kai rahoton lamarin sashin 'yan sandan Umunneochi, inda ta kara da cewar an kama wanda ake zargin.
Chinaka ta ce:
"Eh, mun samu wani rahoto a sashin Umunneochi.
"An kama wanda ake zargin kuma yanzu haka an mika lamarin zuwa sashin binciken laifuka na jihar don gudanar da bincike.
"Za a gurfanar da shi a kotu bayan nan."
Matashi ya kashe mahaifinsa a Filato
A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta kama wani matashi dan shekara 29 mai suna, Joseph Yakubu, wanda ake zargi da kashe mahaifinsa, Yakubu Dalyop.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, ƴan sandan sun kama matashin ne bisa zargin ya buga wa mahaifinsa taɓarya, kuma daga karshe rai ya yi halinsa.
Kwamishinan ƴan sandan jihar Filato, Hassan Steve Yabanet, ne ya sanar da hakan a hedkwatar ƴan sanda ranar Talata.
Asali: Legit.ng