Bola Tinubu Ya Kai Ziyara Fadar Fitaccen Sarki, Ya Yi Magana Mai Jan Hankali Kan Gwamnan da Ya Rasu

Bola Tinubu Ya Kai Ziyara Fadar Fitaccen Sarki, Ya Yi Magana Mai Jan Hankali Kan Gwamnan da Ya Rasu

  • Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci mai martaba basaraken Owo, Oba Ajibade Gbadegesin Ogunoye, domin yi masa ta'aziyyar rasuwar Akeredolu
  • Shugaban ƙasar ya bayyana tsohon gwamnan a matsayin mayaƙi mara tsoro wanda zai yi wahala a iya cike giɓin da ya bari
  • Ya ce wannan rashi ne da zai zaburar da sauran al'umma domin su zauna da kowa lafiya kuma su yi hidima ga mutane

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce zai yi wahala a iya cike gurbin da marigayi tsohon gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, ya mutu ya bari.

Shugaba Tinubu ya kara da cewa kyawawan ayyukan da Akeredolu ya bari ba zasu taɓa gushewa ba har abada, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya kama hanyar zuwa ta'aziyyar gwamnan APC da ya rasu, bayanai sun fito

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Tinubu Ya Ziyarci Basaraken Owo, Ya Ce Da Wuya A Cike Gurbin Akeredolu Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Bola Tinubu ya yi wannan furucin ne yayin da ya ziyarci fadar sarkin Owo, Olowo na Owo, Oba Ajibade Gbadegesin Ogunoye, domin ta'aziyyar rasuwar Akeredolu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Tinubu ya faɗa game da tsohon gwamnan Ondo?

Shugaban ƙasar ya ce abun farin ciki ne mutum ya bar duniya a daidai lokacin da aka fi yawan yabonsa.

A rahoton Channels tv, Tinubu ya ce:

"Wannan kaɗai ya kamata ya zaburar da mu, mu riƙa rayuwa da manufa, mu tashi tsaye wajen cimma burikanmu kuma mu bar ayyukan alherin da mutane za su riƙa tuna mu da su.
"(Akeredolu) ya nuna jarumtaka da rashin tsoro musamman a kokarin kafa shugabanci na gari. Zan iya kwatanta shi da mayaƙi mara tsoro, ba za a taɓa mantawa da shi ba wajen kyautata rayuwar al’ummarsa.”

A nasa bangaren, Oba Ogunoye, ya bayyana marigayi Akeredolu a matsayin dan dimokradiyya na gaskiya wanda ke da kishin kasa da bin ka’idoji.

Kara karanta wannan

"A ƙara haƙuri" Abu 1 da aka buƙaci Shugaba Tinubu ya yi domin magance tsadar rayuwa a Najeriya

Jiga-jigan da suka raka Tinubu zuwa Owo

Shugaba Tinubu ya samu rakiyar Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo da Gwamnan jihar Ekiti, Abiodun Oyebanji zuwa fadar basaraken Owo yau Laraba.

Sauran waɗanda suka raka shi sun haɗa da mataimakin gwamnan Ondo, Olayide Adelami, kakakin majalisar dokoki, Olamide Oladiji, da dai sauransu.

Shaibu ya tada rigima da sakatariyar PDP

A wani rahoton kuma Mataimakin Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya dira sakateriyar PDP ta ƙasa da ke Abuja ranar Laraba, 28 ga watan Fabrairu, 2024.

Philip Shaibu ya buƙaci a ba shi satifiket na shaidar zama ɗan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar PDP a zaben jihar Edo mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262