Shugaba Tinubu Ya Kama Hanyar Zuwa Ta'aziyyar Gwamnan APC da Ya Rasu, Bayanai Sun Fito

Shugaba Tinubu Ya Kama Hanyar Zuwa Ta'aziyyar Gwamnan APC da Ya Rasu, Bayanai Sun Fito

  • Bola Ahmed Tinubu ya kama hanyar zuwa Ondo domin yin ta'aziyyar tsohon gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu, wanda aka ɓinne shi ranar Jumu'a
  • Rahoto ya nuna cewa bayan ta'aziyya ga iyalansa, shugaban ƙasar zai ziyarci Sarkin Owo da kuma shugaban kungiyar yarbawa
  • Rotimi Akeredolu ya mutu ne a watan Disamba, 2023 yana da shekaru 67 a duniya bayan fama da jinya ta tsawon lokaci a ƙasar Jamus

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Yanzu haka ana tsammanin Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na dab da sauka a jihar Ondo domin yin ta'aziyyar rasuwar tsohon gwamna, Rotimi Akeredolu.

Shugaba Tinubu zai kai wannan ziyara ta ta'aziyya ne ga iyalan tsohon gwamnan na jam'iyyar APC a garin Owo da ke jihar a Kudu maso Yammacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya kai ziyara fadar fitaccen Sarki, ya yi magana mai jan hankali kan gwamnan da ya rasu

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Tinubu Zai Kai Ziyara Gidan Tsohon Gwamnan APC da Ya Mutu a Ondo Hoto: Ajuri Ngelale, Rotimi Akeredolu
Asali: Twitter

Shugaban kasa zai ziyarci fadar sarkin Owo

Jaridar Punch ta tattaro cewa Bola Tinubu zai kuma kai ziyarar girmamawa ga fitaccen sarkin nan, Olowo na Owo, Oba Ajibade Ogunoye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan haka kuma shugaban kasar zai ziyarci jagoran ƙungiyar kare al'adun yarbawa, Afenifere, Cif Reuben Fasoranti a Akure, babban birnin jihar Ondo.

Ana sa ran shugaban ƙasa zai je wannan ziyara ne tare da rakiyar gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, da kuma wasu daga cikin shugabannin APC na ƙasa da na jihar.

Tuni dai aka ga wasu daga cikin jiga-jigan ƙungiyar yarbawa Afenifere sun nemi wuri sun zauna a gidan Fasoranti suna dakon isowar mai girma shugaban ƙasa, Bola Tinubu.

An tsaurara matakan tsaro

Bugu da ƙari, an ƙara gurke tarin jami'an tsaro dauke da kayan aiki kuma cikin shiri a birnin Akure da Owo a shirye-shiryen zuwan shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Mataimakin gwamna ya ƙara tada rigima, ya dira sakateriyar PDP ta ƙasa kan muhimmin abu 1

Wannan na zuwa ne kwanaki ƙalilan bayan an ɓinne tsohon Gwamna Akeredolu ranar Jumu'a da ta gabata a mahaifarsa watau Owo, rahoton The Nation.

Mataimakin shugaban ƙasa, Ƙashim Shettima da shugaban APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje na cikin manyan mutanen da suka halarci jana'izar.

Jigon APC ya nemi a ƙara hakuri da Tinubu

A wani rahoton kun ji cewa Wani jigon jam'iyyar APC ya buƙaci ƴan Najeriya su kara haƙuri ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, domin nan gaba zasu ci moriyarsa.

Anthony Adefuye ya kuma shawarci Tinubu ya gaggauta sanar da mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata domin kuɗi su wadata a hannun jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262