Rashin Tausayi: An Kama Wani Matashi da Ake Zargin Ya Halaka Mahaifinsa Kan Abu 1 a Arewa
- Yan sanda sun kama wani matashi ɗan shekara 29 a duniya bisa zargin ya halaka mahaifinsa a Jos, babban birnin jihar Filato
- Rahoto ya nuna matashin mai suna, Joseph Yakubu, ya ɗauki taɓarya ya maka wa mahaifinsa a kai bayan sun samu wani ɗan saɓani
- Kwamishinan ƴan sandan Filato, Hassan Steve Yabanet, ya ce da zaran sun gama bincike kan lamarin, zasu gurfanar da wanda ake zargi a gaban ƙuliya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jos, jihar Plateau - Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta kama wani matashi dan shekara 29 mai suna, Joseph Yakubu, wanda ake zargi da kashe mahaifinsa, Yakubu Dalyop.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta tattaro, ƴan sandan sun kama matashin ne bisa zargin ya buga wa mahaifinsa taɓarya, kuma daga karshe rai ya yi halinsa.
Kwamishinan ƴan sandan jihar Filato, Hassan Steve Yabanet, ne ya bayyana haka yayin da yake nuna wanda ake zargin a hedkwatar ƴan sanda ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa matashin ya kashe ubansa?
CP ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da mahaifin da wanda ake zargin ɗansa suka yi ja-in-ja, kuma ba zato ba tsammani ya dauki taɓarya ya maka masa ita a kai.
Kwamishinan ƴan sandan ya yi bayanin cewa lamarin ya afku ne ranar 15 ga watan Fabrairu, 2024 a Kambel da ke yankin Anglo-Jos.
A cewarsa, wani maƙocin gidan da abun ya faru ne ya kai rahoton lamarin ga ƴan sanda na caji ofis din Anglo-Jos ranar 20 ga watan Fabrairu, 2024.
Wane mataki ƴan sanda suka ɗauka?
CP Yabanet jami'an ƴan sanda sun samu rahoton faruwar lamarin ne bayan magidancin ya mutu a asibitin jihar Filato na musamman inda aka kwantar da shi.
Kwamishinan ƴan sandan ya ce tuni aka kama wanda ake zargin yayin da aka ajiye gawar mahaifinsa a dakin ajiyar gawarwaki na Asibitin.
Ya ƙara da cewa da zaran an kammala bincike da tattara dukkan bayanai, zasu gurfanar da matashin a gaban kotu, Premium Times ta tattaro.
Ƴan sanda sun ceto mutum 40
A wani rahoton kuma Yan sanda da taimakon mafarauta sun yi nasarar halaka ƴan bindiga masu yawa tare da ceto mutane 40 da aka yi garkuwa da su a Taraba.
Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP David Iloyanomon, ya ce jami'an tsaro sun ragargaji ƴan bindiga, sun kamo 10 daga cikinsu.
Asali: Legit.ng