Majalisa Na Shirin Cafke Gwamnan CBN Kan Abu 1, Bayanai Sun Fito
- Rashin amsa gayyatar da kwamitin majalisar wakilai ya yi wa gwamnan CBN, ya sanya ya samu barazanar samun sammaci
- Kwamitin majalisar kan asusun jama'a ne ya yi wannan barazanar bayan Olayemi Cardoso ya ƙi bayyana a gabansa
- Kwamitin dai ya gayyaci Cardoso ne domin ya zo ya yi bayani kan yadda kudaɗe ke zurarewa ta hanyar Remita
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Kwamitin majalisar wakilai kan asusun jama'a ya yi barazanar bayar da sammacin kama gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Oluyemi Cardoso, saboda ƙin amsa gayyatar da ya aike masa.
Shugaban kwamitin, Bamidele Salam (PDP, Oyo), ya yi wannan barazanar a wata wasiƙa da ya aikewa Mista Cardoso a ranar Talata, 27 ga watan Fabrairun 2024, cewar rahoton Premium Times.
A cikin wasiƙar mai ɗauke da kwanan watan 27 ga watan Fabrairu, kwamitin ya zargi gwamnan na CBN da yin watsi da gayyatar da aka yi masa don jin ta bakinsa kan yadda kuɗaɗe ke zurarewa ta Remita.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mista Salam ya ce gwamnan babban bankin na CBN ya yi watsi da gayyata guda huɗu, amma ya aika da wakili ne kawai ya bayyana a madadinsa.
Majalisa ta yi barazanar cafke Cardoso
Ya yi barazanar cewa kwamitin zai yi amfani da sashe na 89 na kundin tsarin mulki na shekarar 1999, wanda ya umurce shi da ya bayar da sammacin kamu idan buƙatar hakan ta taso.
Wnai ɓangare na sanarwar na cewa:
"Har ila yau, yana da kyau ka sani cewa kwamitin a ƙarƙashin sashe na 89 (1) (d), yana da ikon bayar da takardar sammaci don tirsasa halartar duk wanda bayan an kira shi ya bayyana, ya gaza, ya ƙi ko ya yi sakacin yin haka.
"Rashin amsa wannan gayyata na iya barin kwamitin ba tare da wani zaɓi ba illa bayar da sammacin kama ka kamar yadda doka ta tanada."
Wane wa'adi kwamitin ya ba Cardoso?
Mista Salam ya ce Gwamnan CBN na da wa’adin mako guda ya bayyana a gaban kwamitin ko kuma ya fuskanci sammacin kama shi daga majalisar, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.
Sashi na 89 ya bai wa majalisar wakilai ikon bayar da sammacin kamawa don tirsasa bayyana a gabanta don gudanar da bincike.
Majalisa Ta Kafa Kwamitin Bincike Kan Bashin Buhari
A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dattawa ta kafa kwamitin da zai binciki bashin N30trn da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ciwo.
Tsohon shugaban ƙasan dai ya ciwo bashin ne daga wajen babban bankin Najeriya (CBN) a lokacin mulkinsa.
Asali: Legit.ng