Daga Karshe Shugaba Tinubu Ya Bayyana Dalilin da Ya Sa Ya Tsige Tallafin Man Fetur
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce matakin cire tallafin man fetur abu ne mai cike da ƙalubale
- Sai dai shugaban ya ce matakin ya zama wajibi domin tabbatar da tsaron makamashi na dogon lokaci da kuma bunƙasar tattalin arziƙin ƙasar nan
- Bayan da Tinubu ya janye tallafin man fetur, farashin man fetur ya tashi a Najeriya, ƙasar da ta fi kowacce ƙasa haƙo mai a Afirika
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a ranar Talata, 27 ga watan Fabrairu ya bayyana cewa matakin da ya ɗauka na cire tallafin man fetur abu ne mai cike ƙalubale.
Tinubu, ya ce ya zama dole don tabbatar da samar da ɓangaren makamashi wanda yake da gaskiya da riƙon amana.
Tinubu, wanda ya yi magana a wajen buɗe taron ƙasa da ƙasa kan makamashi na Najeriya (NIES) na shekarar 2024 a Abuja, ya amince cewa matakin ya janyo wahalhalu musamman a tsakanin masu ƙaramin karfi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ba da tabbacin cewa a ƙarshe tattalin arziƙin zai inganta kuma amfanin hakan zai bayyana, jaridar Vanguard ta ruwaito.
Meyasa Tinubu ya cire tallafin man fetur?
Tinubu wanda ya samu wakilcin Mohammed Idris, ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na ƙasa, ya bayyana cewa tsaron makamashi shine fifikon gwamnatinsa.
Ya bayyana cewa:
"Ta hanyar cire tallafin, muna samar da wani fannin makamashi mai gaskiya da riƙon amana. Kuɗaɗen da aka ware a baya don bayar da tallafi kan albarkatun man fetur yanzu an karkatar da su zuwa haɓaka makamashinmu da sauran abubuwan more rayuwa.
"Bugu da ƙari kuma, cire tallafin ya ƙarfafa ci gaban kamfanoni masu zaman kansu a cikin masana'antar makamashi, tare da yiwuwar jawo ƙarin masu zuba jari na gida da na waje.
"Matakin cire tallafin man fetur ba abu ne mai sauƙi ba, amma abu ne da ya zama dole domin ɗorewar tsaron makamashi da ci gaban tattalin arziƙin ƙasarmu da muke so.
"Ina kira ga masu ruwa da tsaki, ciki har da masana a masana'antu, masu tsara manufofi, da sauran jama'a, da su shiga tattaunawa mai ma'ana da haɗin gwiwa yayin da muke cikin waɗannan lokutan ƙalubale amma masu kawo sauyi."
FG Za Ta Bada Tallafin N25,000
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta shirya fara bada tallafin N25,000 ga iyalai miliyan 15 a faɗin ƙasar nan.
Tallafin za a bayar da shi domin rage raɗaɗin da ƴan Najeriya suke ciki sakamakon taɓarɓarewar tattalin arziƙi.
Asali: Legit.ng