"Sai Mun Ga Bayansu": Sunday Igboho Ya Fadi Muhimmin Abu 1 da Ya Dawo da Shi Najeriya

"Sai Mun Ga Bayansu": Sunday Igboho Ya Fadi Muhimmin Abu 1 da Ya Dawo da Shi Najeriya

  • Cif Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho ya ce ba shi da sauran wani abu da yake tsoro bayan rasuwar mahaifiyarsa
  • Mai fafutukar ya ce ya dawo ne domin ƙwato ƙasar Yarabawa daga hannun makiyayan da ke kai wa mutanensa hari suna kashe su
  • Igboho ya buƙaci wasu da su haɗa kai da shi wajen ƴantar da ƙasar Yarabawa daga hannun makiyayan da ke mamaye gonakinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Igboho, jihar Oyo - Ɗan rajin kare haƙƙin Yarabawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya ce ya dawo Najeriya ne domin fatattakar makiyaya masu kisa daga ƙasar Yarabawa.

Igboho ya ce sojoji da ƴan sandan da aka tura zuwa yankin Yarabawa ba za su iya kare al’ummar yankin Kudu maso Yammacin ƙasar nan daga makiyaya ba.

Kara karanta wannan

Hukumar NDLEA ta yi kamu mafi girma a tarihinta, bayanai sun fito

Sunday Igboho ya gargadi makiyaya
Sunday Igboho ya ja kunnen makiyaya Hoto: @AlarmeeThe75076
Asali: Twitter

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga wasu jama'a a cikin harshen Yarabanci a yayin jana'izar mahaifiyarsa a mahaifarsa, Igboho a jihar Oyo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai fafutukar ya ce ba shi da wani abin tsoro kasancewar mahaifiyarsa ba ta da rai.

Wacce buƙata Sunday Igboho ya nema?

Ya buƙaci sauran da su yi aiki tare da dattawa domin kare wuraren su daga hannun makiyaya, jaridar The Punch ta ruwaito.

A kalamansa:

“Ina so ku tsaya tare da ni domin mu ƴantar da kanmu daga makiyayan da ke mamaye filayenmu. Mu tabbatar da tsaro a dukkan ƙasashen Yarabawa da kanmu, idan ba haka ba, za su ƙwace mana filayenmu.
"Bai kamata mu jira gwamnati ko wani ba. Mu yi aiki tare. Ba za mu iya noma a filayenmu ba saboda waɗannan makiyaya.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Mataimakin gwamnan PDP ya bankado wata sabuwar makarkashiya da aka shirya masa

Ya ƙara da cewa:

"Mahaifiyata ce ta kasance abin tsorona a baya amma yanzu ta tafi, babu abin da zan sake jin tsoro. Yanzu na dawo don ƙwato mana ƙasarmu.”

Sunday Igboho Ya Zargi Buhari

A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan fafutukar kare haƙƙin Yarabawa Sunday Igboho ya zargi tsohon shugaban kasa da kashe mahaifiyarsa da kuma kanwarsa.

Igboho ya ce tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ne sanadin kisan mahaifiyar tasa inda ya zargi cewa ya yi yunkurin ganin bayansa shi ma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng