Wata Sabuwar Zanga-Zanga Ta Barke a Sakatariyar Jam’iyyar APC Kan Wani Dalili 1 Tak
- Magoya bayan ɗan takarar gwamnan jihar Edo, Dennis Idahosa sun gudanar da zanga-zanga a babbar sakatariyar jam'iyyar APC da ke Abuja
- Masu zanga-zangar sun nemi Abdullahi Umar Ganduje da ya rushe zaben fidda gwani da aka sake yi a jihar wanda ya ba Okpebola nasara
- A cewar masu zanga-zangar, an tafka kura-kurai a zaben, kuma an soke zaɓen farko ne kawai don a nuna Okpebola jam'iyyar ke so ba Idahosa ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Masu zanga-zangar maza da mata a ranar Litinin, sun mamaye hedikwatar jam’iyyar All Progressives Congress ta kasa dake babban birnin tarayya, Abuja.
Sun gudanar da zanga-zangar ne domin nuna rashin jin dadinsu kan sakamakon zaben fidda gwani na gwamna da jam’iyyar ta kammala a jihar Edo.
Sanata Monday Okpebolo ne ya lashe zaben fidda gwani da jam'iyyar ta gudanar domin fuskantar zaben gwamnan jihar da za a yi a ranar 21 ga Satumba, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masu zanga-zangar na goyon bayan Dennis Idahosa
The Punch ta rahoto cewa masu zanga-zangar, wadanda ke goyon bayan Dennis Idahosa, daya daga cikin ’yan takara 11 da suka sha kaye, sun yi zargin cewa zaben fidda gwani na cike da kura-kurai.
Sun tare babbar kofar sakatariyar jam’iyyar, tare da bukatar ganawa da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Ganduje, domin neman a yi musu adalci.
Yayin da suke daga kwalaye daban-daban na zanga-zangar, sun yi zargin cewa ba a bi tsarin mulkin jam’iyyar ba wajen gudanar da zaben fidda gwani na jihar.
Bukatar masu zanga-zangar ga jam'iyyar APC
Sannan sun yi kira ga kwamitin ayyuka na kasa na jam'iyyar da ya dawo da zaben fidda gwani na farko da aka yi aranar 17 ga watan Fabrairu, kamar yadda Sahara Repoters ta ruwaito.
A zaben ne aka ayyana Idahosa da wasu ’yan takara biyu a matsayin wadanda suka lashe zaben, lamarin da ya tilasta wa shugabannin jam’iyyar bayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba.
Sai dai magoya bayan Idahosa sun yi iƙirarin cewa an nemi a sake zaɓen ne kawai domin nuna goyon baya ga Okpebolo, wanda aka ayyana a matsayin wanda ya lashe zaɓen da aka sake.
Masu zanga-zaga sun mamaye majalisar dokokin tarayya
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa masu zanga-zaga daga ƙungiyar ƴan ƙwadago (NLC) sun mamaye ginin majalisar dokokin tarayya a ci gaba da zanga-zangar adawa da tsadar abinci.
Joe Ajaero, shugaban kungiyar NLC na kasa ya yi nuni da cewa sun isa ginin majalisar ne don isar da kokensu ga shugaban majalisa, Akpabio
Asali: Legit.ng