Kotu Ta Ba MTN, Airtel da Glo Umarnin Abin da Za Su Yi da Layukan da Ba Su da NIN
- Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas ta haramtawa kamfanonin sadarwa na Airtel, MTN da sauran su rufe layukan mutane
- Dan rajin kare hakkin dan adam, Olukoya Ogungbeje ne ya yi karar gwamnati, babban lauyan tarayya da kuma ministan shari’a, MTN da Airtel
- Kamfanonin sadarwa a kasar sun yi barazanar rufe layukan mutanen da ba su hada layukan su da lambar shaidar kasa (NIN) ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Ikeja, jihar Legas - An haramta wa Airtel, MTN da sauran kamfanonin sadarwa rufe duk wani layin waya wanda ba a hada shi da lambar shaidar dan kasa (NIN) ba.
Mai shari’a Ambrose Lewis-Allagoa na babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas ya ba da umarnin a ranar Litinin, 26 ga watan Fabrairu, inji rahoton Vanguard.
Hukuncin dai ya samo asali ne daga bukatar wani mai fafutukar kare hakkin bil adama, Olukoya Ogungbeje na neman dakatar da kamfanonin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilan Ogungbeje na neman dakatar da kamfanonin
Lauyan a karar da ya gabatar, ya roki kotun ta dakatar da hukuncin da mai shari’a Lewis-Allagoa ya yanke a ranar ranar 8 ga Mayu, 2023, domin tuni ya daukaka kara don ci gaba da sauraron shari'ar.
Kamar yadda Daily Independent ta ruwaito, Ogungbeje ya lissafa dalilai guda 10 na neman takardar da wancan hukuncin suka hada da:
"Tauye hurumin shari'a na kotun da tsarin shari'ar Najeriya wanda kuma ya tauye hakkin wanda ya shigar da karar.
"Cewa wannan kotun mai alfarma a cikin kyakkyawan hukunci da ta yanke a ranar 8 ga Mayu 2023 ta kori sammacin mai kara na farko.
Ogungbeje bai gamsu hukuncin ba, ya daukaka kara
Sauran dalilan sun hada da:
“Cewa wanda ya yi karar bai gamsu da wannan hukuncin ba, ya yi amfani da ‘yancin daukaka kara da kundin tsarin mulki ya ba shi ta hanyar gabatar da sanarwar daukaka kara a ranar 26 ga watan Yuli 2023."
“Cewa karar da mai shigar da kara ya daukaka ta shafi dukkanin bangarorin da ke kunshe cikin hukuncin wannan kotun mai daraja.
“Cewa wadanda ake kara suna sane da daukaka karar da shigar da karar ya yi zuwa kotun daukaka kara ta Najeriya, tun da an ba su kwafi na takardar karar."
Yadda ake hada NIN da MTN, Airtel
A baya Legit Hausa ta rahoto cewa daukacin kamfanonin sadarwa a Najeriya sun nemi kwastomominsu da su hada NIN dinsu da layukan wayarsu domin kaucewa rufe wa.
Wannan ya biyo bayan umarnin da hukumar kula da shaidar dan kasa (NIMC) ta ba kamfanonin, wanda Legit ta yi bayanin yadda ake hada NIN da layukan waya.
Asali: Legit.ng