An Kama Mutane 3 Kan Zargin Tayar Da Zaune Tsaye a Kano

An Kama Mutane 3 Kan Zargin Tayar Da Zaune Tsaye a Kano

  • Rundunar 'yan sandan Kano ta ce ta kama wasu mutum uku da suka yi yunkurin tayar da zaune tsaye a tsohuwar kasuwar 'yan magani
  • Kwamishinan'yan sandan jihar, Hussaini Gumel ya ce mutanen sun yi yunkurin fasa shaguna don satar kayan 'yan kasuwar amma aka kama su
  • Rundunar ta rarraba jami'anta zuwa tsohuwar kasuwar da sabuwar don tabbatar da cewa an ba da tsaro da dakile barayin kayan mutane

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kano - Rundunar 'yan sanda ta kama wasu mutum uku da suka yi yunkurin tayar da zaune tsaye yayin da yan kasuwar magani suka fara kwashe kayan su zuwa sabuwar kasuwar KEC.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar Kano, CP Hussaini Gumel ya ce an kama masu laifin ne lokacin da ake rufe kantin Mai-Karami, Kano, lokacin da yan kasuwar ke kwashe kayan su.

Kara karanta wannan

Bayan jami'an sun kashe shugabannin 'yan bindiga, tsageru sun afkawa mutane a Kaduna

Yan sanda sun dakile yunkurin satar kaya a Kasuwar Magunguna ta Kano.
Yan sanda sun dakile yunkurin satar kaya a Kasuwar Magunguna ta Kano. Hoto: @KanoPoliceNG
Asali: Twitter

Yan sanda sun tsaurara tsaro a kasuwar magani

Gumel ya bayyana cewa mutanen ukun sun yi yunkurin tayar da tarzoma da nufin dauke hankalin jama'a don fasa shagunan tare da satar kaya, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan ya ce wadanda ake zargin yanzu haka suna hannun ‘yan sanda, inda ya kara da cewa ya bayar da umarnin ba da 'cikakken tsaro a kasuwar”.

Ya zuwa yanzu dai akwai tsaro a tsohuwar kasuwar da sabuwar yayin da 'yan kasuwar ke ci gaba da kwashe kayansu, bayan samun umarni daga kotu.

Farashin kayan abinci ya karye a kasuwar Kano

A wani labarin daga jihar Kano, kungiyar 'yan kasuwar abinci ta Dawanau ta ce mambobinta sun karya farashin kayan abinci don saukakawa mutane halin da ake ciki.

Shugaban yan kasuwar, Alhaji Muttaka Isah ya ce ciniki ya yi kasa sosai a kasuwar, ga kuma karancin kudi a hannun jama'a da tsadar da kaya suka yi, wanda ya tilasta karya farashin kayan.

Yanzu dai farashin buhun masara ya koma naira dubu 53 sabanin yadda yake a baya akan naira dubu 60. Haka kuma buhun dawa yanzu ya sauka zuwa naira 49,000, sabanin naira 55,000 da ake sayar da shi a baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.