Jerin Kasashen Nahiyar Afirka 10 da Aka Fi Dauke Wutar Lantarki da Yawan Daukewar a Shekara
Najeriya na daga cikin kasashen Nahiyar Afirka da suka fi fuskantar matsalar wutar lantarki a yankin.
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Tun shekaru da dama da suka wuce wutar ke cikin wani yanayi wanda har zuwa yanzu an gagara shawo kan matsalar.
Masana sun tabbatar da cewa wutar lantarki kusan ita ce hanyar farfado da tattalin arziki wanda idan babu za a iya samun matsala.
Legit Hausa ta jero muku kasashe 10 da aka fi yawan dauke wutar lantarki a Nahiyar Afirka da aka fitar daga 2014 zuwa 2022.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Najeriya
Rahoton Cobiyar Utility Bidder a Burtaniya ya tabbatar da cewa a Najeriya ana dauke wutar har sau 394 a duk shekara.
Wannan dauke wutar da ake yi a Najeriya shi ne mafi muni a Nahiyar a matsayinta na wacce ake yi wa lakabi da giwar Afirka.
2. Afirka ta Tsakiya
Wannan kasa da ke yankin Nahiyar Afirka ta Tsakiya da aka fi sani da Central African Republic ta kasance a mataki na biyu a jerin kasashen 10 inda ake daukewa sau 349.
3. Benin
Kasar Benin da ke makwabtaka da Najeriya ta kasance a mataki na uku inda ake dauke wutar sau 336 a cikin shekara daya.
4. Nijar
Kasar Nijar ita ma da ke makwabtaka da kasar Najeriya ta na fama da matsalar inda ake daukewa sau 264 a shekara.
5. Congo
Kasar Congo wacce ke jerin kasashe masu tasowa a Nahiyar ana dauke wutar sau 258 a shekara.
6. Gambia
Kasar da ake kira The Gambia ta kasance a mataki na shida inda ake dauke wutar sau 253 a cikin shekara, cewar Aminiya.
7. Burundi
Kasar na daga cikin kananan kasashe da ke fama da matsalar yayin da ake dauke wutar sau 199 a cikin shekara.
8. Zambia
Kasar da ke mataki na takwas na fuskantar matsalar wanda ya ke jawo matsalar tattalin arzikin kasar, ana dauke wutar sau 160.
9. DR Congo
Jamhuriyar Dimukradiyya ta Congo ta kasance a mataki na tara inda ake dauke wutar har sau 148 a shekara.
10. Burkina Faso
Kasar da ke mataki na 10 a cikin jerin kasashen ita ce Burkina Faso wacce ke hannun sojoji, ana dauke wutar sau 118 a cikin shekara guda.
Minista ya bukaci cire tallafin wuta
Kun ji cewa, Ministan Makamashi, Adebayo Adelabu ya ce gwamnati ba za ta iya ci gaba da biyan kudin tallafin wuta ba.
Adelabu ya ce akwai yiwuwar su cire tallafin wutar saboda basukan da kamfanonin ke bi.
Asali: Legit.ng