Gwamnoni 5 da suka yi kaca-kaca da mataimakansu, suka nakasa su a siyasance

Gwamnoni 5 da suka yi kaca-kaca da mataimakansu, suka nakasa su a siyasance

A tarihin siyasar Najeriya, an saba arangama tsakanin gwamnoni da mataimakansu.

Abinda yasa hakan ke yawan faruwa kuwa bai wuce dalili daya ba. Da yawa daga cikin gwamnonin ba a bin zabinsu yayin tsayawa takara. Jam'iyyar siyasar ce ke tsayar musu da abokin takara.

A wasu lokutan kuwa, ana samun rikici tsakanin gwamna da mataimakinsa ne idan mataimakin ya fara zargin ana wareshi a al'amuran shugabancin. Abinda da yawan gwamnoni ke yi.

Amma a lokuta da yawa, gwamnonin ke yin nasara a rikicin inda suke tube mataimakinsu daga kujerunsu tare da lalata duk wasu burikansu na siyasa.

Ga jerin gwamnoni a Najeriya da suka yi kaca-kaca da mataimakansu sannan suka illata burinsu na siyasa.

1. Tinubu da Akerele-Buchnor (1999-2003)

Mutum na farko a wannan jerin shine shugaban jam'iyyar APC kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu da tsohon mataimakinsa Kofoworola Bucknor-Akerele. Bucknor-Akerele da Tinubu sun yi fadan da yasa dole yayi murabus.

Kamar yadda tace, rikicin ya fara ne a yayin da Tinubu ya so kwace jam'iyyar gaba daya. Ta yi murabus ne lokacin da fadan ya tsananta kuma aka fara birne-birne a ofishinta.

2. Tinubu da Pedro (2003-2007)

Karo na biyu da Tinubu yayi kaca-kaca da mataimakinsa kenan. A lokacin da ya zarce mulkin jihar Legas ya dauka Olufemi Pedro wanda aka fi kira da Femi a matsayin mataimakinsa.

Rikicin ya fara ne gabanin zaben 2007. Pedro ya so gadar kujerar Tinubu amma shugaban APC sai ya ce Babatunde Raji Fashola yake so. Hakan ne kuwa yasa suka fara rikici wanda a 2007 aka tsige Pedro daga kujerarsa. Fadansa da Tinubu ya nakasa duk wani burinsa na siyasa.

Gwamnoni 5 da suka yi kaca-kaca da mataimakansu, suka nakasa su a siyasance
Gwamnoni 5 da suka yi kaca-kaca da mataimakansu, suka nakasa su a siyasance
Asali: UGC

KU KARANTA: Yadda matar aure ta yi wa tsohuwar budurwar mijinta tsirara tare da tura mata kwalba a gaba

4. Rochas Okorocha da Madumere

Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya yi wani babban rikici da mataimakinsa Eze Madumere.

Madumere da wasu sun soki bukatar Okorocha na saka sirikinsa Uche Nwosu don maye gurbinsa. Wannan rikicin ya sa aka tsige Madumere a 2018.

4. Yahaya Bello da Simon Achuba

Gwamnan Yahaya Bello da mataimakinsa Simon Achuba sun yi kaca-kaca inda duk wani burin siyasa na Achuba ya tashi a tutar babu.

Achuba ya zargi ubangidansa da rashin hakuri a kan sukar ra'ayinsa da yake yi.

Daga bisani majalisar jihar ta tsige Achuba a 2019.

A watan Fabrairun 2020, wata babbar kotun tarayya da ke jihar ta soke tsige mataimakin da aka yi.

5. Rotimi Akeredolu da Agboola Ajayi

Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya yi rikici da mataimakinsa wanda daga bisani mataimakin ya koma jam'iyyar adawa ta PDP.

Duk da barin jam'iyyar APC da mataimakin gwamnan yayi, Ajayi ya dauka alkawarin cewa ba zai yi murabus ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel