Tsadar Rayuwa: Gwamnan APC Ya Goyi Bayan Tinubu, Ya Abu 1 da Ya Kamata 'Yan Najeriya Su Yi
- Gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji ya buƙaci ƴan Najeriya su yi wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu addu'a
- Oyebanji ya bayyana cewa halin tabarbarewr tattalin arziƙin da ake ciki a ƙasar ɓan ba laifin shugaban ƙasan ba ne
- Ya bayyana cewa wahalhalun da ake ciki a ƙasa, nan ba da jimawa ba za a ga ƙarshensu idan an yi haƙuri
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Ekiti - Biodun Oyebanji, gwamnan jihar Ekiti, ya ce nan ba da jimawa ba za a kawo ƙarshen matsalolin tattalin arziƙi da ƙasar nan ke fama da su.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wajen taron yabo da addu’o’i na wata-wata da aka gudanar a ɗakin taro na Lady Jibowu, gidan gwamnati, a Ado-Ekiti babban birnin jihar, cewar rahoton TheCable.
Oyebanji, ya ce ba Shugaba Bola Tinubu ne ya haddasa tabarbarewar tattalin arziƙin da ƙasar nan ke fuskanta ba, rahoton The Punch ya tabbatar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ƙara da cewa shugaban ƙasar yana aiwatar da tsare-tsare da manufofin da suka dace da mutane domin sauƙaƙa wahalhalu.
Wane kira Oyebanji ya yi ga ƴan Najeriya?
Oyebanji ya roƙi ƴan Najeriya da su yi haƙuri su yi wa shugaban ƙasan addu’a.
A kalamansa:
"Ina so in ƙarfafa mana gwiwa a yau a matsayinmu na bayin Allah don mu ci gaba da yin imani ga Allah kuma mu ƙara yawan addu'o'inmu ga Najeriya, jihar Ekiti da kuma shugaban ƙasa.
"Na fahimci halin da muke ciki, amma gaskiyar magana ita ce ba shugaban ƙasa ne ya haddasa wadannan rikice-rikice ba amma Allah ya shirya shi kan irin wannan lokaci. Abin da yake buƙata shi ne goyon bayanmu, addu’o’inmu da fahimtarmu.
"Ina roƙon mu cewa shugaban ƙasa yana buƙatar taimakonmu, yana buƙatar addu’o’inmu, kada mu yi wani abu da zai karya masa ƙwarin gwiwa."
Sarkin Musulmi Ya Shawarci 'Yan Najeriya
A wani labarin kuma, kun ji cewa mai alfarma Sarkin Musulmi ya shawarci ƴan Najeriya kan daina cin mutuncin shugabanni.
Mai alfarma Sarkin Musulmin ya bayyana cewa abin da ƴan Najeriya ya kamata su riƙa yi wa shugabanni shi ne addu'a ba cin mutunci ba.
Asali: Legit.ng