Obasanjo Ya Yi Sabuwar Fallasa Kan Adadin Man Fetur Din da Ake Sacewa a Najeriya
- Tsohon shugaban ƙasa, Oluesegun Obasanjo ya faɗi irin ɓarnar da ake yi wa tattalin arziƙin ƙasar nan
- Obasanjo ya bayyana cewa sama da kaso 80% na ɗanyen man fetur ɗin Najeriya sace ake yi
- A cewar Obasanjo daga cikin ganga miliyan abu na man fetur da ake samarwa a ƙasar nan, ana sace sama da ganga miliyan 1.7m
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya ce sama da kaso 80% cikin kaso 100% na ɗanyen man fetur na Najeriya sace shi ake yi.
Jaridar Vanguard ta ce Obasanjo ya bayyana haka ne a Abuja a wajen ƙaddamar da wani littafi mai suna, ‘Court and Politics’ wanda Dr. Umar Ardo, wanda tsohon na hannun daman tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ne ya rubuta.
A cewar tsohon shugaban ƙasan, ɗaya daga cikin dalilan da suka sa tattalin arziƙin Najeriya ya lalace shi ne yayin da sauran ƙasashe masu arzikin man fetur ke da tarihin adadin man da suka haƙo, Najeriya ba za ta iya lissafin nata ba saboda sata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gangar man fetur nawa ake sacewa a Najeriya?
Obasanjo wanda ya samu wakilcin tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu, ya ce satar ɗanyen mai na ɗaya daga cikin dalilan da zai sa tattalin arzikin Najeriya ya lalace.
Tsohon shugaban ƙasan ya ce yayin da adadin ɗanyen mai ya kai kusan ganga miliyan biyu a kowace rana, sama da ganga miliyan 1.7 ake sacewa, rahoton Thisday ya tabbatar.
Akan ko Najeriya za ta koma kan tsarin firaminista, Obasanjo ya ce babu laifi a tsarin shugaban ƙasa, inda ya ce ƴan Najeriya ba sa bin doka da oda.
Gwamnatin Tinubu Za Ta Raba Tallafi
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta shirya fara rabon. N25,000 ga ƴan Najeriya.
Ministan kuɗi Wale Edun shi ne ya bayyana hakan, inda ya ce iyalai 15m ne za su amfana da tallafin da za a raba.
Ya bayyana cewa za a ɗauki tsawon wata uku ana bayar da tallafin wanda ƴan Najeriya 75m za su amfana da shi.
Asali: Legit.ng