Adaidaita Ya Kai Miliyan 2.6 Yanzu”: Matashi da Ya Je Shagon Adaidaita Ya Koka Saboda Tsadarsa
- Wani 'dan Najeriya da ya je shagon siyar da adaidaita sahu ya yi bidiyo don ya koka kan tsadar adaidaita a yanzu
- A wani bidiyo da ya yadu a TikTok, mutumin ya ce naira miliyan 2.6 ake siyar da shahararriyar abun hawa nan na adaidaita
- Ya alakanta tsadar adaidaita da karancin dala sannan ya koka cewa akwai alamun farashin zai ci gaba da hawa
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura
Wani mutumi ya kadu matuka yayin da ya je shagon siyar da adaidaita sahu inda aka fada masa farashin sa naira miliyan 2.6.
Ya ce abun bakin ciki ne cewa adaidaita yana neman ya fi karfin wasu mutane yanzu a Najeriya.
A wani bidiyo da @unclenasco ya wallafa a TikTok, mutumin ya ce ya je shagon domin ya tsayawa wani da ke son siyan adaidaita a bashi a matsayin jingina.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce ya ki tsaya masa bayan ya ji farashin adaidaitan saboda ba shi da tabbacin ko direban zai iya biyan irin wannan makudan kudi.
Ya rubuta:
"A yanzu ana siyar da keken adaidaita kan naira miliyan 2.6 sannan dala daya 1,800 ne yanzu. Abubuwa suna kara tabarbarewa ne a kullun. Shin haka za mu ci gaba?"
Mutumin ya alakanta tsadar keken da rashin dala da rikicin canji a Najeriya.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
@Agbawo ya ce:
"Menene a jikin adaidaita da ba za mu iya kerawa a Najeriya ba? Lokaci ya yi da za mu koma kere-kere."
@Narsty1120 ya ce:
"Na siya keke kan miliyan 1.2 a 2022."
@Ken ya ce:
"Na siya wannan keken a farashi mai tsada a 2020 a kan 630k."
@Genuis_Starseed ya ce:
"Makonni biyu da suka wuce ana siyar da siminti 5,800; a yau 11,500. Samun dala a lokacin da siyar da shi yanzu zai baka karfin siya iri daya."
Za a kaddamar da keke mai aiki da lantarki
A wani labarin kuma, mun ji cewa wani kamfanin sufuri na Najeriya, mai suna Egoras Technology, ya kaddamar da adaidaita sahu mai aiki da iskar gas da fetur.
Shugaban kamfanin, Ugoji Harry, ya bayyana cewa an samar da adaidaita sahun ne domin magance matsalar da cire tallafin mai da aka yi a Najeriya ya haifar.
Asali: Legit.ng