An Tsige Kakakin Majalisa a Wata Jihar Arewa Saboda Babban Dalili 1

An Tsige Kakakin Majalisa a Wata Jihar Arewa Saboda Babban Dalili 1

  • Mambobin majalisar Zamfara sun tsige kakakin majalisar dokokin jihar, Hon. Bilyaminu Moriki
  • Kamar yadda rahotanni suka zo, tsige Moriki ya zama dole ne sakamakon yawan hare-haren ta'addanci a jihar
  • 'Yan majalisar jihar sun nada Hon. Bashar Gummi a matsayin kakakin majalisa na wucin gadi domin ya maye gurbin Moriki

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Jihar Zamfara - Majalisar dokokin jihar Zamfara ta tsige kakakinta, Bilyaminu Moriki, sannan ta nada Bashar Gummi a matsayin kakakin majalisa na wucin gadi.

Hakan ya biyo bayan kudirin da 'dan majalisa mai wakiltar mazabar Maru, Nasiru Abdullahi ya gabatar, inda mambobi 18 cikin 24 suka amince da shi.

An maye gurbin kakakin majalisar da na wucin gadi
An Tsige Kakakin Majalisa a Wata Jihar Arewa Saboda Babban Dalili 1 Hoto: Zamfara State House of Assembly
Asali: Facebook

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, mambobin majalisar 18 daga cikin 24 sun amince da tsige kakakin yayin wani taron gaggawa da suka gudanar a daren Alhamis, 22 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Dakarun noma: Gwamnati ta dauki mataki 1 na tsare manoma daga farmakin 'yan bindiga

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar mambobin majalisar, an dakatar da kakakin majalisar ne saboda matsalar tsaro da ke addabar jihar da tare da majalisar ta yi wani yunkuri na dakatar da annobar ba.

'Yan majalisar sun bukaci a sabon kakakin majalisar da aka nada da ya yi amfani da matsayinsa wajen kawo karshen ‘yan bindiga da suka kusan gurgunta tattalin arziki a jihar.

'Dan majalisa ya nemi a kara daukar mataki kan rashin tsaro

Daya daga cikin 'yan majalisar, Shamsudeen Basko, mai wakiltar mazabar Talata Mafara, ya yi jan hankali ga sabon kakakin majalisar.

Basko ya bayyana cewa batun rashin tsaro na daya daga cikin muhimman batutuwan da ya kamata a bai wa fifiko wanda ya sa aka dakatar da tsohon kakakin, rahoton Blueprint.

Basco ya ce:

“Ina da batutuwa guda biyu, amma an yi nazari a kan daya, wato na rashin tsaro da ke damun jama’armu. A kullum ana kashe mutanenmu ana garkuwa da su.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Benue za ta kori Fulani makiyaya daga jihar ta kan wani dalili 1 tak

“Me muke yi a majalisa?, ya kamata mu tashi mu yi wani abu don kare mutanenmu.
"Hakan ya klasance ne saboda ‘yan bindigar da ke dauke da makamai suna mamaye hedikwatar kananan hukumomin ba tare da fuskantar kalubale ba.
"Ya kamata mu yi kira ga gwamnati da ta dauki mataki a yanzu don kare al’ummarmu.”

An bukaci gwamnan Zamfara ya tashi tsaye

A wani labarin kuma, mun ji cewa kwanan nan gwamnatin Zamfara a karkashin Dauda Lawal tayi hobbasa wajen magance matsalar rashin tsaro da ke jihar.

Kafin tafiya tayi nisa, an fara zargin Askarawa watau jami’an tsaron sa-kai da aka kafa da hannu wajen mutuwar wani Bawan Allah.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng