'Yan Bindiga Sun Tafka Sabuwar Ta'asa a Jihar Arewa

'Yan Bindiga Sun Tafka Sabuwar Ta'asa a Jihar Arewa

  • Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun yi ajalin wani jami'in hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) a jihar Sokoto
  • Ƴan bindigan waɗandan suka tare hanya sun kuma yi garkuwa da wasu mutum uku bayana halaka jami'in hukumar ta NDLEA
  • Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Sokoto ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce jami'in ƴan sanda sun bi sahun ƴan bindigan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Wasu ƴan bindiga sun harbe wani jami’in hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) har lahira a Sokoto.

Miyagun ƴan bindigan sun kuma yi garkuwa da mutum uku a hanyar zuwa filin jirgin sama na Sultan Abubakar III da ke Sokoto, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi kwantan ɓauna, sun kashe babban ɗan sanda yana tsaka da aiki a jihar PDP

'Yan bindiga sun kai hari a Sokoto
'Yan bindiga sun halaka jami'in NDLEA a Sokoto Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Wani mazaunin yankin wanda ɗansa na cikin waɗanda aka kama, Muhammad Baba Usman, ya ce ƴan bindigan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 9:30 na dare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Su huɗu ne, dukkansu riƙe da bindigogi. A mota suka zo wacce suka ajiye a gefen titi. Suna fitowa suka fara harbe-harbe. Wani mutum wanda harsashi ya same shi ya rasu a hanyar zuwa asibiti.
"Sun kuma yi awon gaba da wasu mutum uku ciki har da ɗana. Har yanzu muna jiran kiran nasu domin sanin buƙatunsu."

Me hukumomi suka ce kan lamarin?

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Sokoto, ASP Ahmed Rufa’i, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Kakakin ya bayyana cewa marigayin jami’in hukumar NDLEA ne da ke kan hanyarsa ta komawa cikin babban birnin jihar.

A cewar Rufa’i, ƴan sanda na bin sahun maharan domin cafko su.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Ƴan sanda sun bayyana mummunan laifin da ya sa aka kama shugaban LP na ƙasa

Jihar Sokoto dai na daga cikin jihohin Arewacin Najeriya masu fama da matsalar rashin tsaro.

Ƴan Bindiga Sun Kai Hari a Benue

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai sabon harin ta'addanci a wasu ƙauyukan jihar Benue.

Ƴan bindigan a yayin harin sun halaka mutum ɗaya tare da raunata wani daban. Hakazalika a yayin harin ƴan bindigan sun ƙona gidaje masu yawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng