Mutum 1 Ya Mutu Yayin da Aka Kaure Tsakanin Hausawa da Yarbawa a Legas, Bayanai Sun Fito

Mutum 1 Ya Mutu Yayin da Aka Kaure Tsakanin Hausawa da Yarbawa a Legas, Bayanai Sun Fito

  • Wani mutum ya rasa ransa yayin da wasu suka jikkata bayan an kaure tsakanin Hausawa da Yarbawa a jihar Legas
  • Lamarin ya faru ne a daren jiya Alhamis 22 ga watan Faburairu yayin da wani mai suna Abbey ya yi kokarin raba Hausawa fada
  • Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Benjamin Hundeyin bai ce komai ba game da rikicin a kasuwar Oluwole

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas - An samu raunuka da mutuwar wani bayan rikicin kabilanci ya barke tsakanin Yarbawa da Hausawa a jihar Legas.

Harkokin kasuwanci sun tsaka cak da safiyar yau Juma'a 23 ga watan Faburairu a kasuwar Oluwole da ke Ogba a karamar hukumar Ojodu.

Kara karanta wannan

Kwastam ta fara raba wa talakawan Najeriya kayan abinci da ta kwace, ta fadi ka'idojin cin gajiyar

Wani ya mutu yayin rikici tsakanin Hausawa da Yarbawa a Legas
Rikicin ya faru ne da tsakar daren jiya Alhamis a cikin kasuwa. Hoto: Babajide Sanwo-Olu.
Asali: UGC

Menene dalilin rikicin a jihar Legas?

Lamarin ya faru ne a daren jiya Alhamis 22 ga watan Faburairu yayin da wani mai suna Abbey ya yi kokarin raba Hausawa fada.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin da ya jawo wani da ba a bayyana ba ya daba masa wuka wanda hakan ya bar shi cikin jini a wurin.

Daily Trust ta tabbatar da cewa daga bisani Abbey ya ce ga garinku wanda ya jawo daukar fansa daga Yarbawa.

Rikicin ya jawo asarar dukiya da faffasa kayayyakin Hausawa da ke siyar da albasa da tattasai da sauransu.

Martanin 'yan sanda kan rikicin

An gano jami'an tsaro su na sintiri a wurin don tabbatar da samar da tsaro da kare lafiyar al'umma, cewar Tori News.

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Benjamin Hundeyin bai ce komai ba game da rikicin da ya faru a Legas.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Jirgi maƙare da mutane ya gamu da mummunan hatsari a jihar APC, rai ya salwanta

Da aka tuntubeshi shi, Hundeyin ya mai da martani ta sakon waya inda ya ce ba zai iya daukar waya ba a halin yanzu.

Jirgin ruwa ya kife da jama'a da dama

A baya, mun kawo muku labarin cewa Wani jirgin ruwa da ya dauko fasinjoji 17 ya gamu mummunan hatsari a yankin Ikoyi da ke jihar Legas.

Lamarin ya faru ne a ranar Laraba 21 ga watan Fabrairu a jihar inda aka tabbatar hadarin ya yi ajalin mutum daya yayin da sauran kuma aka ceto rayuwar wasu.

Rahotanni sun tabbatar da cewa jirgin ruwan ya ci karo ne da wani kwankweren simint a cikin tekun a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.