An Samu Asarar Rayuka Bayan Jami'an Tsaro Sun Yi Kazamin Artabu da 'Yan Ta'adda a Jihar Arewa
- Ƴan ta'adda sun halaka kwamandan rundunar tsaro ta KCWC na ƙaramar hukumar Kankara a jihar Katsina
- Sanusi Hassan ya rasa ransa bayan ya jagoranci tawagarsa zuwa maɓoyar ƴan ta'addan domin fatattakarsu
- A yayin artabun mutum shida suka rasa ransu daga ɓangaren jami'an tsaro yayin da aka halaka ƴan ta'adda 20
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Wasu ƴan ta’adda sun kashe kwamandan rundunar tsaro ta 'Katsina Community Watch Corps' (KCWC) na ƙaramar hukumar Kankara, Sanusi Hassan.
Ƴa ta'addan sun kuma kashe wasu ƴan banga huɗu na yankin da wasu samari biyu ƴan Birdigau a lokacin da suka yi arangama da jami’an tsaro da suka kai farmaki maɓoyar su a Ƴar Taipa, Birdigau ‘J’ da ke tsakanin Malumfashi da Kankara
Yadda lamarin ya auku
Wani jami’in tsaro daga yankin ya shaida wa jaridar Vanguard cewa, jami’an tsaron na cikin wani shiri ne na fatattakar ƴan ta’addan daga sabuwar maɓoyarsu a lokacin da lamarin ya faru.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya biyo bayan rahoton sirri da aka samu cewa jiga-jigan ƴan bindiga, Dankarami da Barbaru sun kafa wata sabuwar maɓoya a Ƴar Taipa.
A cewarsa, ƴan bindigan a baya-bayan nan suna shirin kai hare-hare kan ƙauyukan da ke kusa da maɓoyarsu bayan sun baro cikin daji.
Yayin da jami’an tsaro suka yi wannan rashin, ya ce ƙoƙarin da suka yi ya janyo asarar rayuka masu yawa na ƴan bindigan.
A kalamansa:
"Rundunar ta fuskanci turjiya daga ƴan bindigan yayin da artabun ya yi sanadiyyar mutuwar mutum shida a ɓangaren jami'an tsaro da kuma sama da mutum 20 daga bangaren ƴan ta’addan."
An farmaki ragowar ƴan ta'addan
Majiyar ya kuma bayyana cewa, bayan arangamar da aka yi a ƙasa, an kai wani samame ta sama a makarantar firamare ta Dinary da ke ƙauyen Yargoje, inda aka ce ƴan bindigan da suka gudu sun taru, inda aka kashe waɗanda har yanzu ba a tantance adadinsu ba.
Ya ce harin da aka kai ta sama ya daƙile yunƙurinsu na kwashe gawarwakin ƴan uwansu da suka mutu.
Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani mazaunin garin Ƙankara, mai suna Abubakar Nuhu, wanda ya tabbatar da kisan kwamandan rundunar ta KCWC na Kankara.
Ya bayyana cewa an yi bata kashi sosai da ƴan ta'addan inda aka halaka da dama daga cikinsu, inda ya ce ba a san adadin yawan ƴan ta'addan da aka halaka ba.
Ya bayyana cewa an kwashe dogon lokaci ana artabu tsakanin jami'an tsaron da miyagun ƴan ta'addan.
Ƴan Bindiga Sun Kai Farmaki a Katsina
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki a wasu ƙauyuka guda uku na ƙaramar hukumar Faskari a jihar Katsina.
Ƴan bindigan a yayin farmakin da suka kai sun halaka mutum shida tare da yin awon gaba da wasu mutum 38.
Asali: Legit.ng