Tsohon Shugaban Kasa Ya Fadi Matakin da Ya Kamata 'Yan Najeriya Su Dauka Kan Mulkin Tinubu

Tsohon Shugaban Kasa Ya Fadi Matakin da Ya Kamata 'Yan Najeriya Su Dauka Kan Mulkin Tinubu

  • Janar Yakubu Gowon ya bukaci 'yan Najeriya da su karawa Shugaban kasa Bola Tinubu lokaci ya magance matsalar tattalin arziki da kasar ke fuskanta
  • Da yake magana ga manema labarai bayan ganawar sirri da Tinubu, Gowon ya ce gwamnati na iya bakin kokarinta don inganta Najeriya
  • Gowon ya bayyana cewa babu shugaba da zai tsallake shan suka, amma dai wadanda ke kan ragamar ayyuka ne suka san ainahin yadda abubuwa suke

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Abuja - Tsohon shugaban Najeriya a mulkin soja, Yakubu Gowon ya bukaci 'yan Najeriya da su kara hakuri da Shugaban kasa Bola Tinubu, sannan su kara ba shi lokaci ya magance matsalolin da ke kasar.

Da yake jawabi ga manema labarai bayan ganawa da shugaban kasa a Fadar Shugaban kasa a ranar Laraba, 21 ga watan Fabrairu, Gowon ya ce Tinubu na iya bakin kokarinsa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya shiga ganawar gaggawa da tsohon shugaban kasa a fadarsa, bayanai sun fito

Gowon ya roki 'yan Najeriya da su kara hakuri
Ku Yi Hakuri Ku Karawa Tinubu Lokaci a Samu Abin da Ake So, Gowon Ga ‘Yan Najeriya Hoto; @NGRPresident
Asali: Twitter

Gowon, wanda ya bukaci Tinubu da kada ya damu da sukar da yake sha, ya jaddada muhimmancin samar da sakamako mai kyau, rahoton Arise News.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Channels TV ta nakalto Gowon yana cewa:

"Ina ganin gwamnati na iya bakin kokarinta kan matsaloli daban-daban da kasar ke fuskanta amma a bangaren 'yan Najeriya, kada ka damu, kana iya shan suka, mutanen da ke waje, sun san abin da baka sani ba.
"Ina tunanin ya zama dole 'yan Najeriya su ba shugaban kasar lokaci don ya saita abubuwa. Ya yi wuri da yawa da za a ce za a cimma sakamako yanzu, wannan shine ra'ayina."

Juyin mulki: Gowon ya musanta batun kunyata ECOWAS

Gowon wanda ya kafa kungiyar ECOWAS, ya bayyana cewa ya tattauna da shugaban kasar kan halin da kungiyar ta yammacin Afirka ta shiga kwanan nan.

Kara karanta wannan

Yaron Tinubu ya ji babu dadi daga rokon mutane a yi hakuri da gwamnatin mahaifinsa

“An yi sa’a, a wannan karon ya ba ni damar ganin shi domin tattauna batutuwa daban-daban, musamman batun matsalar da ECOWAS ke ciki a yanzu wanda nake ganin ya kamata a magance.
“Kuma a matsayina na wanda ya tsira daga cikin wadanda suka kafa ta, ina ganin dole ne mu tattauna wasu tsare-tsarensa don ganin abin da za a iya yi don shawo kan lamarin.
"Don haka, wannan shine abin da ya kawo ni nan kuma mun yi tattaunawa mai ma'ana."

Tsohon shugaban kasar ya kuma karyata rahotannin da ya ce ana zarginsa da kin halartar taron manema labarai na kungiyar ECOWAS, wanda hakan ke nuna cewa shi ne ke yi wa kokarin kungiyar zagon kasa.

Ya dage cewa lallai ba haka lamarin yake ba, inda ya kara da cewa mai yiwuwa saboda rashin sadarwa ne amma shugaban kasa ya gaya masa abin da zai yi a wannan taron, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Aiki na shine na biyu mafi wahala a duniya, Gwamnan CBN Cardoso

Ya ce zai kasance a hedkwatar ECOWAS a wannan rana domin gudanar da wasu ayyuka.

Gowon ya shiga ganawar sirri da Tinubu

A baya mun ji cewa Shugaban kasa, Bola Tinubu yanzu haka ya na ganawar sirri da tsohon shugaban kasa da ke birnin Tarayya Abuja.

Tinubu ya na ganawar ce da Janar Yakubu Gowon a fadarsa da ke birnin Tarayya Abuja, cewar The Nation.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng