Bidiyon Matan ‘Yan Boko Haram Da Aka Kama Daga Borno Za Su Koma Wurin Mazajensu a Tafkin Chadi

Bidiyon Matan ‘Yan Boko Haram Da Aka Kama Daga Borno Za Su Koma Wurin Mazajensu a Tafkin Chadi

  • Dakarun tsaro da ke yaki da ta'addanci a yankin Arewa sun yi nasarar kama wasu mata da ake zargin iyalan 'yan Boko Haram ne
  • An kama matan da yara da dama a hanyarsu ta komawa ga mazajensu 'yan ta'adda a Tafkin Chadi bayan sun mika wuya
  • Masanin harkokin tsaro a a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya wallafa bidiyon matan 'yan ta'addan a shafinsa na X

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Dakarun rundunar tsaro sun kama wasu iyalan 'yan ta'addan Boko Haram yayin da suke yunkurin komawa ga mazajensu a tafkin Chadi da Jamhuriyar Nijar.

Shahararren masanin lamuran tsaro a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama, ne ya tabbatar da kamun iyalan 'yan ta'addan a ranar Laraba, 21 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai sabon hari jihar Arewa, sun tafka barna

Dakarun tsaro sun kama matan 'yan Boko Haram
An yi amfani da hoton don misali ne Hoto: Patrick Meinhardt/AFP
Asali: Getty Images

Zagazola Makama ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na X wanda ke nuna matan 'yan ta'addan da aka kama zaune da yara da dama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi wa bidiyon take da:

"Ba za ka iya raba Boko Haram da abubuwa uku ba: Magunguna, kudi da mata."

Kalli wallafarsa da bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani kan kama matan 'yan Boko Haram

@__adewale ya ce:

"Idan an bar ni, wadannan matan abokan harkalla ne."

@I_bayusay ya ce:

"Amma duk da haka gwamnati za ta yake da daukarsu aiki."

@biyids ya ce:

"Basu rantse da Qur'ani ba?"

@vic_shola ya yi martani:

"Wai ta yaya mutanen nan ke rayuwa ne ma?"

@esv_shakur ya ce:

"Duk yadda gwamnati ta yi kokarin shawo kansu sai sun koma ga ayyukansu, gara ma a aika su inda suka cancanta."

Kara karanta wannan

Bayan Murja Kunya, Hisbah ta sake kama wata 'yar TikTok kan babban laifi 1 a Kano

Tsohon gwamnan Neja ya magantu kan Shekau

A wani labarin kuma, tsohon gwamnan jihar Niger, Babangida Aliyu, ya magantu kan yadda aka yi ya raba shugabannin kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau da Abu Qaqa, da jihar a lokacin mulkinsa na farko.

Ya ce wani bangare na magance matsalolin tsaro da suka addabi Najeriya ba komai bane face ta hanyar samar da shiri na musamman don kawo karshen hakan.

A cewarsa, idan za a samu shiri da tsari, za a magance matsalar da ta ingiza yara sama da miliyan 20 da ba sa zuwa makaranta a halin yanzu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng