Wasu Iyalan Boko Haram sun fada hannun Rundunar Sojin Najeriya

Wasu Iyalan Boko Haram sun fada hannun Rundunar Sojin Najeriya

- Sojojin Najeriya sun kama wasu daga cikin Iyalan ‘Yan Boko Haram

- Wani babban Jami’in Sojojin kasar ya bayyana mana wannan a jiya

- Yanzu haka dau mata da wadannan yara su na hannun Sojojin kasar

Mun samu labari a jiya Asabar cewa Rundunar Sojojin Najeriya sun yi ram da wasu Matan ‘Yan ta’aadan Boko Haram a Jihar Borno yayin da su ka tsere daga wani Gari mai suna Mangusun.

Wasu Iyalan Boko Haram sun fada hannun Rundunar Sojin Najeriya
Hotunan wasu yara da matan ‘Yan Boko Haram da aka kama

Wani babban Jami’in Sojojin kasar Birgediya Janar Texas Chukwu ya bayyana cewa wata Runduna ta Operation LAFIYA DOLE ta ci karo da wasu mata da yara da ake zargi na ‘Yan Boko Haram ne yayin da su ke sharan daji.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya baro Landan domin dawowa gida

Rundunar Bataliya ta 25 na Sojojin Operation LAFIYA DOLE sun kama wadannan Bayin Allah ne yayin da su ke kokarin tserewa. Da Sojoji su ka matse su dai sun bayyana cewa su na cikin Iyalan ‘Yan ta’addan Boko Haram.

Yanzu dai wadannan mutane su na hannun Sojojin kasar inda ake cigaba da yi masu tambayoyi. Janar Texas Chukwu ya nemi a yada wannan labari da kuma cigaba da ba Sojojin kasar hadin-kai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel