Sanata Sani ya fadi mafita 1 da Musulmi da Kiristoci Zasu Runguma Domin Farfado da Naira

Sanata Sani ya fadi mafita 1 da Musulmi da Kiristoci Zasu Runguma Domin Farfado da Naira

  • Tsohon 'dan majalisar tarayya Sanata Shehu Sani ya bukaci Musulmai da Kiristocin Najeriya da su nemi taimakon Allah ta hanyar yin addu'a domin farfado da naira
  • Ya bayyana hakan ne yayin da darajar naira ke ci gaba da faduwa a kan darajar Amurka cikin 'yan kwanakin nan
  • Sani ya garzaya shafinsa na X don bayar da shawarar cewa idan har mu'ujizar da ake fatan gani bai faruwa cikin mako guda, to ya kamata mabiya addinan biyu su dukufa yin azumi

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

FCT, Abuja - Tsohon 'dan majalisar tarayya, Sanata Shehu Sani, ya bukaci Kiristoci da Musulmai da su yi wa naira addu'a sakamakon faduwar da ya yi kan dalar Amurka.

Kara karanta wannan

'Dan majalisar tarayya ya soke bikin zagayowar ranar haihuwarsa saboda tsadar rayuwa

A ranar Laraba, 21 ga watan Fabrairu, darajar Naira ta fadi kasa warwas, inda ta kai N1,830 kan dalar Amurka a kasuwar bayan fage.

Shehu Sani ya magantu kan halin da Naira ke ciki
Sanata Sani ya fadi mafita 1 da Musulmi da Kiristoci Zasu Runguma Domin Farfado da Naira Hoto: Shehu Sani/X and Benson Ibeabuchi/Bloomberg
Asali: UGC

Wannan na nuna an samu raguwar kaso 7.10 cikin dari ko N130.00, wanda ya yi rauni fiye da yadda aka rufe a ranar da ta gabata wato kan N1,700.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan koma baya ya nuna tsananin matsalar tattalin arziki da ake fama da shi, inda wannan raguwar ta zama mafi karancin daraja a tarihin naira.

Faduwar darajar naira da ake ci gaba da fuskanta a kasuwar bayan fage yana kara ta'azzara hauhawar farashin kaya, kamar yadda Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta sanar a watan Janairun 2024.

Shehu Sani ya ba Musulmai da Kiristocin Najeriya shawara

Da yake martani kan ci gaban, Sanata Sani ya bayyana cewa lokaci ya yi da ‘yan Najeriya za su koma yin addu’o’i domin kawo karshen halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Sanatoci sun lalubo yadda Gwamnatin Buhari ta haddasa asarar Naira tiriliyan 17

Ya rubuta a shafinsa na X

"Ya kamata Musulmai su yi wa naira addu'a ranar Juma'a mai zuwa. Ya kamata Kiristoci su yi wa Naira addu'a a ranar Lahadi.
"Za ku ga abin al'ajabi a ranar Litinin. Idan ba ku gani ba toh ku yi azumin kwanaki 7 Idan har lokacin ba ku ga abin al'ajabi ba, yana nufin hatta mu'ujiza ta bar ku saboda zunubanku."

Shehu Sani ya yi watsi da zanga-zangar wasu mata

A wani labarin, mun ji cewa al'ummar Najeriya na ci gaba da kowawa saboda tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayan abinci da ake fama da su a bangarori daban-daban na kasar.

Lamarin ya kara muni ne tun bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta yi jim kadan bayan ta garbi ragamar shugabanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng