Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Wata Daliba Ta Dauki Ranta Saboda Dalili 1 Tak
- Wata dalibar jami'a a Ogun ta dauki ranta bayan ta samu labarin cewa ba a tantance kwas din da take karanta ba tsawon shekaru shida
- Jami'ai daga ma'aikatar lafiya ta jihar Ogun da SNMC sun dira a kwalejin kimiyya da kasuwanci ta Harvarde da ke Obada a Abeokuta, babban birnin jihar domin tantancewar
- Jami'an jihar sun rufe tsangayar karatun jinya a makarantar kan hujjar cewa ba a ba makarantar damar karantar da wannan kwas din ba tsawon shekaru shida
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura
Abeokuta, Ogun - Wata dalibar aji uku a tsangayar karatun jinya a kwalejin kimiyya da kasuwanci ta Harvarde, Obada a Abeokuta, jihar Ogun ta dauki ranta.
Dalibar da abin ya ritsa da ita mai suna Ajoke, ta dauki ranta ne bayan samun labarin cewa gwamnatin ta rufe tsangayar da take saboda ba a basu damar karantar da karatun jinya ba.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an gano gawar dalibar ne a dakin kwanan ta da ke wajen makaranta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ma’aikatar lafiya ta jihar Ogun da mambobin kwamitin kula da aikin jinya da ungozoma (SNMC) sun rufe tsangayar karatun jinya na makarantar.
Sun rufe tsangayar ne saboda mallakawa dalibai takardun shaidar kammala karatun jinya tsawon shekaru shida ba tare da SNMC ta tantance su ba.
Dalilin rufe tsangayar karatun jinya na jami'ar Ogun
A yayin da jami'an ke gudanar da aikin a ranar Talata, 20 ga watan Fabrairu, sakataren din-din-din na ma'aikatar lafiya, Kayode Oladehinde ya yi tsokaci kan haka, rahoton Punch.
Oladehinde ya bayyana cewa abin da makarantar ta yi yana daya daga cikin dalilan da yasa ake samun bara gurbi a aikin lafiya, kuma hakan barazana ce ga lafiyar mutane a jihar.
Ya ci gaba da bayyana cewa ba za a bude tsangayar karatun jinya na makarantar ba idan ba a amince da shi ba.
A cewar wakiliyar Oladehinde, Serifat Aminu, mukaddashiyar daraktar kula da ayyukan jinya, duk wani digiri na aikin jinya da aka samu daga kwalejin Harvarde da makarantu masu alaka ba tare da tantancewar NMCN ba zai ci gaba da zama mara amfani.
Aminu ta jaddada cewar za a hana daliban da suka kammala karatu daga irin wadannan makarantu takardar damar aiki a Najeriya da sauran sassa na duniya.
'Daliba ta dauki ranta saboda saurayi
A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa wata dalibar aji hudu a jami’ar jihar Kwara ta dauki ranta sakamakon tangarda da ta samu a harkar karatunta.
An tattaro cewa dalibar mai suna Rashidat Shittu, ta sheke kanta ne gabanin fara jarrabawarsu bayan ta kwankwadi maganin kashe kwari.
Asali: Legit.ng