'Ƴan Bindiga Sun Kai Sabon Hari a Jihar Arewa, Sun Kona Gidaje Masu Yawa

'Ƴan Bindiga Sun Kai Sabon Hari a Jihar Arewa, Sun Kona Gidaje Masu Yawa

  • An shiga jimami a jihar Benue bayan ƴan bindiga sun halaka mutum ɗaya yre da raunata wani daban a wani sabon hari a jihar Benue.
  • Miyagun ƴan bindigan sun kai harin ne a ƙauyen Ikoba na ƙaramar hukumar Apa ya jihar mai fama da matsalar ƴan bindiga
  • A wani harin da ƴan bindigan suka kai a ƙauyen Akpete, sun ƙona gidajen mutane masu yawa a ranar Talata, 20 ga watan Fabrairun 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benue - Rahotanni sun bayyana cewa wasu ƴan bindiga sun kashe mutum ɗaya tare da raunata mutum ɗaya a wani hari da suka kai a ƙauyen Ikobi na ƙaramar hukumar Apa ta jihar Benue.

Jaridar The Punch ta ce harin na zuwa ne mako guda bayan ƴan bindiga sun kashe mutum huɗu a ƙaramar hukumar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai farmaki kan bayin Allah, sun kashe mutane tare da tafka ta'asa mai ban tausayi

'Yan bindiga sun kai hari a Benue
'Yan bindiga sun kona gidaje a yayin sabon harin da suka kai a Benue Hoto: Emmanuel Ter
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa mazauna yankin sun ce ƴan bindigan sun kuma ƙona gidaje a ƙauyen Akpete da misalin ƙarfe 3:00 na yammacin ranar Talata, 20 ga watan Fabrairun 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda lamarin ya auku

Wani mazaunin garin ya bayyana cewa wanda aka kashe mai suna Aminu Akanu, an kashe shi ne a tsakanin Ikobi da Oloba da misalin ƙarfe 5:00 na yammacin ranar Litinin a lokacin da yake dawowa daga Ugbokpo, hedikwatar ƙaramar hukumar Apa.

Ya bayyana cewa waɗanda harin ya ritsa da su, na kan hanyarsu ta komawa gida ne lokacin da aka yi musu kwanton ɓauna aka kai musu hari.

A cewarsa, wanda aka kashe ɗin ya dawo ne daga Legas kwanan nan don ganin tsohuwar mahaifiyarsa a lokacin da ya gamu da ajalinsa.

Legit Hausa ta yi ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Benue, Catherine Anene, kan lamarin, sai dai ba ta ɗauki kiran da aka yi mata ta wayarta ba, sannan ba ta dawo da amsar saƙon da aka tura mata ta waya ba.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da ƴan bindiga suka halaka bayin Allah da yawa a garuruwa 5 a jihar Arewa

Ƴan Bindiga Sun Halaka Mutum 10 a Benue

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun salwantar da rayukan mutum 10 a wani sabon hari a jihar Benue.

Miyagun ƴan bindigan dai sun halaka mutanen ne a hare-haren da suka kai a wasu ƙauyuka guda huɗu na ƙaramar Apa ta jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng