Gwamnati Ta Gaji, Ta Shirya Binciken Bashin N23tr da Emefiele Ya Ba Gwamnatin Buhari
- Ministan tattalin arziki ya ce gwamnatin Bola Tinubu ba za ta yi saurin biyan bashin da CBN ya Najeriya aro a shekarun baya ba
- Wale Edun ya nuna dole sai an binciki kudin da gwamnatin tarayya ta karbi bashi daga babban bankin kafin a fara biyan tukuna
- Gwamnati mai-ci tana kokarin tsaida salon da Muhammadu Buhari ya rika bi wajen samun tiriliyoyin kudi daga Godwin Emefiele
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyanna niyyarta na binciken Naira tiriliyan 23 da babban bankin kasa na CBN ya ba Najeriya aro.
Ministan kudi da tattalin arziki, Wale Edun ya shaida haka a wajen wani taro da ma’aikatarsa ta shirya yau a cewar jaridar Punch.
An yi taro na musamman a kan kula da dukiyar gwamnati a babban birnin tarayya Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnati za ta kara hako danyen mai
Wale Edun ya kuma shaida cewa an bukaci kamfanin NNPCL ya kara adadin danyen man da ake hakowa saboda kudin shiga ya karu.
Ministan ya bayyana niyyar gwamnatinsu na gabatar da kudiri a majalisar tarayya domin a inganta harajin da ake tatsa daga jama’a.
Idan har an soke tsarin afuwar biyan haraji kamar yadda majalisa ta bukata, Edun ya ce za a huta da karbar aron kudi a hannun CBN.
Gwamnatin Najeriya ta ci bashin makudan kudi daga hannun bankin CBN a lokacin Godwin Emefiele, lamarin da aka soka a kasar.
Edun wanda aka nada a Yunin bara ya ce sai sun yi bincike kafin su fara biyan bashin kudin da aka karba daga hannun bankin CBN.
"Babban bankin kasa na CBN ya nuna dole ayi watsi da tsarin ba gwamnati aron kudi kuma abin da muka amince da shi kenan."
"Mun kama hanyar, an gaji kusan N22.7tr da za a biya. Muna bincike, kamar zan biya bashi ne sai in bincika nawa ake bi na."
- Wale Edun
Kwanaki sabon gwamnan CBN, Yemi Cordoso ya tabbatar da za su daina ba gwamnati aro har sai sun dawo da bashin da suka karba.
Majalisa ta ce Buhari ya jawo asara
Ana da labari Sanata Muhammad Sani Musa ya soki afuwar da aka yi wa manyan kamfanoni wajen biyan haraji a shekarun baya.
Kwamitin majalisar dattawa ya ce ya kamata a dakatar da shirin a kawo sabon tsarin karbar haraji ganin FIRS ta rasa kusan N17tr.
Asali: Legit.ng