Tsadar Siminti: Gwamnati Ta Yi Barazanar Daukar Mataki 1 Da Zai Jefa Dangote Da BUA Cikin Matsala
- Gwamnatin tarayya ta ce tana duba yiwuwar bude iyakokin kasar don fara shigowa da siminti da nufin karya farashinsa a kasuwanni
- Wannan gargadi ne da ministan gidaje da raya karkara, Arc. Dangiwa ya yi wa kamfanonin da ke sarrafa siminiti a Najeriya
- Dangiwa ya ce ma damar Kamfanonin suka gaza karya farashin simintinsu, to za su ba da damar shigo da shi daga ƙasashen waje don ya zama gasa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Gwamnatin tarayya ta ce za ta duba yiwuwar bude iyakokin kasar don shigo da siminti idan masu sarrafawa a Najeriya suka ki rage farashin sa a kasar.
Gwamnatin ta ce ba za ta lamunci karin kudin siminiti saboda babu wani sinadarin hada siminti da ake amfani da dala wajen sayo shi, The Nation ta ruwaito.
Gwamnati ta soki dalilan kamfanonin na kara farashi
Ministan gidaje da raya karkara, Arc. Ahmadd Dangiwa, ya ce kayan hada simitin da suka hada da limestone, laka, kasar silica da gypsum dukkansu a Najeriya ake samun su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dangiwa ya bayyana hakan a ranar Talata, 20 ga wata a Abuja, a wani taron gaggawa da gwamnati ta gudanar da masu kamfanonin sarrafa siminiti a kasar.
Ya ce bai kamata kamfanonin su fake da kudin iskar Gas ba saboda shi ma a Najeriya ake samun sa, kuma babu uzuri na cewar kudin hakar sinadarai sun karu.
Ministan ya ce tun farko an hana shigo da siminti Najeriya saboda ba kamfanonin cikin gida damar fadada kasuwancin su.
Gwamnati ta yabawa kamfanin BUA
Amma ya ce idan gwamnatin ta bude iyakokin kasar aka fara shigo da siminti gadan-gadan, watakila hakan zai ankarar da kamfanonin irin illar da za su fuskanta.
Dangiwa ya kuma ba su misali da kamfanin BUA wanda ya ce a shirye yake ya karya farashin siminiti zuwa naira dubu bakwai.
Da wannan ya ce bai ga dalilin da zai sa sauran kamfanonin su ƙi amince da rage farashin su ba kamar yadda BUA ya yi alkawari.
Gwamnati za ta kafa kwamitin daidaita farashin siminti
Dangiwa ya fadawa kamfanonin cewa:
"Ba Najeriya ce kadai ke fuskantar matsalolin da kuka zayyana ba, hasali ma wasu sun zarce namu, amma matsayin masu kishin kasa, dole mu saukakawa mutane.
"Ya zama wajibi ku yi karatun ta-nutsu domin gwamnati ta hana shigo da siminti saboda a taimake ku, yanzu kuma muna da bukatar naku taimakon."
Tun da fari, shugaban sashen kasuwanci na kamfanin simintin Dangote, Rabiu Umar ya dora alhakin tashin farashin siminiti akan karin kudin gas da kayan aiki.
A karshe dai ministan ya ce gwamnati za ta kafa kwamiti da zai duba yiwuwar kayyade farashin siminiti da nufin karya farashinsa a kasuwa.
Masu sarrafa siminti sun gindiya sharuda kan rage farashi
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa kamfanonin da ke sarrafa siminti sun kafa wa Shugaba Tinubu sharuda kafin su rage farashin simintin.
Shugaban kungiyar masu sarrafa simintin, David Iweta ya nemi Tinubu da ya dawo da dokar da tsohon shugaban kasa, marigayi Umaru Musa Yar'adua ya kafa akan samar da siminti.
Asali: Legit.ng