Gwamnan jihar Jigawa na farko a mulkin soji ya rasu

Gwamnan jihar Jigawa na farko a mulkin soji ya rasu

Gwamnan jihar Jigawa na farko a mulkin soji, Olayinka Sule, ya rasu ranar Lahadi yana da shekaru 72 a duniya.

Sule, tsohon birgediya janar a rundunar sojin Najeriya, ya zama gwamnan jigawa na farko bayan kirkirar jihar a watan Agusta na shekarar 1991 a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida.

Ya jagoranci gwamnatin jihar har zuwa watan Janairu na shekarar 1992, lokacin da ya mika mulki zuwa gwamnatin farar hula ta farko a Jigawa a karkashin tsohon gwamnan jihar Jigawa, Barista Ali Sa'ad BirninKudu, lokacin janhuriya ta uku.

Gwamnan jihar Jigawa na biyu a janhuriya ta hudu, Sule Lamido, ne ya sanar da mutuwar marigayin Sule a cikin wani jawabi da kakakinsa, Mansur Ahmad, ya fitar.

Sule Lamido ya bayyana marigayi Sule a matsayin dattijon arziki da ba za a maye gurbin rashinsa ba.

Ya yi addu'ar Allah ya ji kansa, ya yi masa sakayya da gidan Aljannatul Firadus.

Gwamnan jihar Jigawa na farko a mulkin soji ya rasu
Marigayi Olayinka Sule
Asali: Twitter

A dan takaitaccen lokacin da ya shugabanci jihar Jigawa, marigayi Sule ya saka tubalin aiyukan raya garin Dutse, babban birnin jihar Jigawa, da suka hada da saka tubalin fara gina gidaje 1000 a unguwannin Takur da Yadi.

DUBA WANNAN: Bayan ya kwanto ruwa, Mailafia ya yi murabus daga NIPPS, ya fadi dalili

Marigayi Sule ya taba rike babban kwamanda (GOC) a barikin soji ta farko da ke Kaduna a 1996, shekarar da ya yi ritaya daga aikin soja.

Duk da Sule Lamido ya bayyana cewa marigayi Sule ya mutu ne a ranar 23 ga watan Agusta, har yanzu gwamnatin jihar Jigawa ba ta fitar da wani jawabi dangane da mutuwarsa ba a matsayinsa na daya daga cikin tsofin gwamnonin jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel