Magani a gonar yaro: Magungunan cutuka 7 da Zobo ke yi ga dan Adam

Magani a gonar yaro: Magungunan cutuka 7 da Zobo ke yi ga dan Adam

Zobo sanannen abun sha ne a duk fadin duniya kuma ana yawan amfani da shi a matsayin magani. Zobo na da suna kala-kala a wasu sassan duniya.

Ita dai launin zobo ja ne amma mai duhu. Yana da tsami a dandano saboda hakan ne ake abun sha mai tsami da shi. Yana da kamshi mai matukar kayatarwa.

Zobo na da matukar amfani ga lafiyar jikin dan Adam tare da zama magani ga cutuka kamar hawan jini, yawan sinadarin cholesterol, cushewar ciki, inganta garkuwar jiki da sauransu.

Zobo yana maganin cutukan hanta a dan Adam tare da rage yuwuwar kamuwa da cuta daji. Yana inganta lafiya tare da rage kiba ga masu ita.

Yana kunshe da sinadarin Vitamin C da sauran sinadaran da ke saukar da damuwa tare da hawan jini.

Ga wasu cutuka da zobo ke magani:

1. Sauke hauhawar jini

Shan zobo na sauke jini idan ya hau ga masu cutar hauhawar jini. A wani bincike da Odigie IP suka yi a kan abubuwan da ke rage cutar hawan jini tare da bada kariya a kan ciwon zuciya, an gano zobo na kunshe da sinadaran.

2. Rage yawan Cholesterol

Zobo na kunshe da sinadarin da ke rage Cholesterol, hakan na taka rawa wajen bada kariya ga cutukan zuciya tare da bude hanyoyin jini. Zobo na da matukar amfani ga masu ciwon sukari.

Magani a gonar yaro: Amfanin 7 na zobo ga lafiyar jikin dan Adam
Magani a gonar yaro: Amfanin 7 na zobo ga lafiyar jikin dan Adam. Hoto daga The Pulse
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Bangaren Abiola Ajmobi sun yi watsi da taron NEC na APC

3. Kariya daga cutukan hanta

Bincike ya nuna cewa zobo na kunshe da sinadarin da ke maganin ciwukan hanta. Duk wani matacciyar kwayar halitta mara amfani a jiki na fita bayan an sha zobo.

4. Sinadarin bada kariya daga cutar kansa

Zobo na kunshe da protocatechic acid wanda ke kashe kwayar cutar kansa. Zobo na hana girman duk wata kwayar halitta ta kansa.

5. Kashe kwayar cutar bacteria

Zobo na kunshe da ascorbic acid wanda aka fi sani da Vitamin C, babban sinadarin da jiki ke bukata don inganta garkuwa daga cutuka. Ana amfani da shi wurin maganin zazzabi.

6. Maganin ciwon mara a yayin al'ada

Zobo na rage ciwon mara yayin al'ada. Yana saisaita ciwon yayin da yake rage duk wasu alamun na al'ada da suka hada da fushi, damuwa da yawan cin abinci.

7. Maganin rage damuwa

Zobo na dauke da sinadarai masu rage damuwa. Shan zobo na kwantar da hankali tare da rage damuwa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng