An Zo Wurin: Tinubu Ya Waiwayi Talakawa, Ya Tsara Yi Wa Kayan Abinci Farashi

An Zo Wurin: Tinubu Ya Waiwayi Talakawa, Ya Tsara Yi Wa Kayan Abinci Farashi

  • Gwamnatin Najeriya ta ce ta shirya tsaf don kayyade farashin kayan abinci a kasar yayin da hauhawar farashin kayan abinci ke kara kamari
  • Ministan noma da tsaron abinci, Abubakar Kyari, ne ya bayyana hakan a kwanan nan kuma ya ce an nome karin filaye
  • Ministan ya jaddada cewa an nome fili da girmansa ya kai kimanin hekta 150,000 a jihar Jigawa da ke Arewa maso Yamma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Abuja - Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewar ta kammala shirye-shirye don kayyade farashin kayan abinci a kasar.

Ministan noma da tsaron abinci, Abubakar Kyari, ne ya bayyana hakan a babban birnin tarayya Abuja.

Tinubu zai kayyade farashin kaya
An Zo Wurin: Tinubu Ya Waiwayi Talakawa, Ya Tsara Yiwa Kayan Abinci Farashi Hoto: NESG
Asali: Twitter

Kyari ya kuma yi karin haske kan ayyukan gwamnatin Najeriya don rage tsadar abinci a Najeriya.

Kara karanta wannan

An maida motocin abinci 50 Najeriya, za su shiga kasar Nijar bayan umarnin Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin tarayya ta fara noman alkama

Kyari ya bayyana cewa an yi wa manoma rijista saboda noma rani ta shirin bunkasa noman kasa (NAGS-AP), cewa an nome fili mai girman hekta 120,000 na alkama a jihar Jigawa karkashin shirin bankin AfDB.

Ya ce:

"Za a noma sama da hekta 150,000 a karkashin shirin shinkafa, masara inda za a kara manoma kusan 300,000 yayin da kungiyoyi masu zaman kansu na duniya za su bayar da kudade don rage farashin."

Ministan ya bayyana cewa, za a jero kayan abinci na kasashen waje a kan iyakokin kasa domin dakatar da bakin haure, inda ya jaddada cewa fitar da abinci yana amfanar Najeriya amma yana da illa idan gwamnati ba ta amfana da shi.

Jaridar ThisDay ta rahoto cewa Kyari ya bayyana cewa ma'aikatar ta yi umurnin raba tan 42,000 na kayan hatsi ga masu karamin karfi, don rage matsalar hauhawan farashin abinci da karancinsa.

Kara karanta wannan

Ku bamu kwana 30, Masu sarrafa siminti sun gindaya sharuda ga Tinubu kan farashin, sun kawo mafita

Haka kuma, gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi ya sanar da shirin noma hekta 150,000 na alkama a kakar noma mai zuwa don bukasa taron abinci a jihar da kasa baki daya, rahoton Leadership.

Farashin abinci ya tashi yayin da ake fama da tsadar rayuwa

A cewar ministan, za a daidaita aikin noma don kara yawan abincin da ake nomawa, sannan za a rage asarar da ake samu bayan girbi.

Ci gaban na zuwa ne a daidai lokacin da farashin kaya da na ayyuka suka yi tashin gwauron zabi a fadin kasar sakamakon tsadar rayuwa da ake ciki.

Hukumar Kididdiga ta Najeriya (NBS) ta bayyana cewa hauhawar farashin kaya a kasar ya kai kashi 29.90 cikin dari a watan Janairun 2024.

NBS ta ce hauhawar farashin kayan abinci ya shafe sama da kashi 30 cikin dari na alkaluman hauhawar farashin kaya.

Kabiru Gombe ya aikawa Tinubu sako

Kara karanta wannan

Aiki na shine na biyu mafi wahala a duniya, Gwamnan CBN Cardoso

A wani labarin, Sheikh Kabir Muhammad Haruna Gombe wanda babban malami ne a Najeriya, ya aika sako zuwa ga Bola Ahmed Tinubu.

Sheikh Kabir Muhammad Haruna Gombe ya yi magana ne duba da irin halin da al’umma su ke ciki, Legit ta samu bidiyon a shafin X.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng