Tashin Hankali Yayin da Ƴan Bindiga Suka Halaka Bayin Allah da Yawa a Garuruwa 5 a Jihar Arewa

Tashin Hankali Yayin da Ƴan Bindiga Suka Halaka Bayin Allah da Yawa a Garuruwa 5 a Jihar Arewa

  • Ƴan bindiga da ake zaton miyagun fulani makiyaya ne sun kashe mutum 10 a kauyuka 5 da ke ƙaramar hukumar Apa a jihar Benuwai
  • Mazauna garin sun bayyana cewa maharan sun farmaki kauyukan lokaci guda kwanaki uku bayan abinda ya auku a Imana
  • Shugaban ƙungiyar ci gaban Apa ya tabbatar da faruwar lamarin yayin da rundunar ƴan sanda ta ce ba ta sami rahoto ba har yanzu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Benuwai - Rahotanni sun bayyana cewa aƙalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu a wasu sabbin hare-hare da ƴan bindiga suka kai kauyuka huɗu a jihar Benuwai.

Kamar yadda Daily Trust ta tattaro, hare-haren sun shafi ƙauyuka huɗu na gundumar Ikobi da ke ƙaramar hukumar Apa a jihar ta Arewa maso Tsakiya.

Kara karanta wannan

Kwamandojin ƴan ta'adda 3 da wasu mayaƙa 22 sun baƙunci lahira a Borno

Sufetan yan sanda na kasa, IGP Kayode.
Mshara Sun Halaka Rayuka 10 a Kauyuka da Dama a Jihar Benue Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Mazauna kauyukan sun bayyana cewa hare-haren sun auku ne a lokaci guda bayan mummunan harin farko da ƴan bindiga suka kai kauyen Imana a makon jiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanai sun nuna cewa a harin da aka kai kauyen Imana, ƴan ta'addan sun yi ajalin mutane huɗu.

Yadda mahara suka tarwatsa mutane

Ɗaya daga cikin mazauna yankin, wanda ya yi gudun hijira sakamakon sabbin hare-haren, ya faɗa wa ƴan jarida cewa an gano gawarwakin mutum 9 kafin ya baro yankin.

Ya ce:

"Mutum tara aka kashe kwanaki uku bayan harin da aka kai Ibele, Ochumekwu da Ijaha. Miyagun makiyaya sun matsa wajen kai hari kan mutanen mu cikin mako biyun nan.
"Sun jima suna aikata ta'addanci a kan mu, a yanzu da nake magana da ku babu kowa a garin Ikobi kuma garin yana da mutane akalla miliyan ɗaya amma duk sun gudu, sun nemi mafaka a Ugbokpo."

Kara karanta wannan

Ana fama da yunwa ƴan bindiga sun ƙona kayan abinci, gidaje da shanu, sun tafka ɓarna a Arewa

Adadin mutum nawa aka kashe a harin?

Shugaban kungiyar ci gaban Apa, Barista Eche Akpoko, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kara da cewa an gano ƙarin gawar mutun ɗaya bayan gawarwaki 9 da aka gano a farko.

Ya ce an kashe mutane biyar a Ijah-Ibele, uku a Ochumekwu yayin da sauran biyun aka kashe su a kauyukan Adija da Kano.

Sai dai kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Binuwai, SP Catherine Anene, ta ce ba ta da rahoton abin da ya faru a yanzu, rahoton Sahara Reporters.

An yi asarar kayan abinci masu yawa a Neja

A wani rahoton kuma Ƴan bindiga sun kai farmaki ƙauyen Allawa da ke ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Neja, sun tafka mummunar ɓarna ranar Lahadi

Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun ƙona gidaje akalla 30 da kayan binci, kana suka yi awon gaba da mutane masu yawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262