'Yan Bindiga Sun Sace Gawa da 'Yan Uwan Mamacin, Sun Bukaci a Ba Su N50m
- Wasu miyagu ɗauke da bindigu sun yi garkuwa da wata gawa tare da masu rakiyarta a jihar Enugu da ke Kudancin Najeriya
- Ƴan bindigan dai sun sace gawar ne lokacin da aka yi jigilarta daga Legas zuwa Nsukka domin binne ta
- Ƴan uwan mamacin da aka sace gawarsa sun bayyana cewa ƴan bindigan sun buƙaci a ba su N50m kafin su sako mutanen
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Enugu - Ƴan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da gawar marigayi Ugwuanyi Israel daga Ameze Owerre, a yankin Umabor na ƙaramar hukumar Nsukka ta jihar Enugu.
Ana jigilar gawar marigayin ne daga Legas zuwa Nsukka domin shirye-shiryen binne shi lokacin da aka yi garkuwa da shi.
Lamarin ya faru ne a kan titin Mile 9 a ƙauyen Umuoka ƙaramar hukumar Udi ta jihar Enugu, cewar rahoton jaridar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan bindigan ba kawai sun ɗauki gawar Ugwuanyi ba ne, sun kuma yi awon gaba da duk ƴan uwansa da ke tare da shi.
Ƴan uwan mamacin, waɗanda ke jigilar gawar Ugwuanyi zuwa gida, sun faɗa hannun masu garkuwa da mutanen ne bayan sun yi musu kwanton ɓauna, rahoton jaridar The Sun ya tabbatar.
Wata majiya mai tushe daga iyalan mamacin ta bayyana cewa:
“Gawarsa na kan hanyarta ne daga Legas a jiya (Lahadi) lokacin da masu garkuwa da mutane suka tsayar da motar da ke dauke da gawarsa, sannan suka yi garkuwa da mutanen da ke cikin motar tare da direban a ƙaramar hukumar Umuoka Udi ta jihar Enugu."
Na wa ƴan bindigan suke so a ba su?
An tattaro cewa tun daga lokacin masu garkuwa da mutanen sun tuntuɓi danginsa inda suka buƙaci a biya su kuɗin fansa Naira miliyan 50.
Majiyar ta ci gaba da cewa:
"Da safiyar ranar Litinin suka kira mu domin mu nemo naira miliyan 50.
"Tsoron mu shine kada gawar ta ruɓe kafin su sake su. Ba mu san abin da za mu yi ba saboda mutanenmu da ke Legas sun kashe maƙudan kuɗaɗe a kan rashin lafiyar Israel."
Legit Hausa ta yi ƙoƙarin jin ta baki kakakin rundunar ƴan sandan jihar Enugu kan aukuwar lamarin, sai dai bai dawo da amsar saƙon da aka tura masa ta wayarsa ba.
Ƴan Bindiga Sun Kai Hari a Zamfara
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari a hedikwatar ƴan sanda da ke ƙaramar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.
Ƴan bindigan a yayin harin sun halaka mutum ciki har da wani jami'in ɗan sanda tare da tafka ɓarna mai yawa a garin.
Asali: Legit.ng