Rudani Yayin Da Shahararriyar 'Yar Tiktok, Murja Kunya, Ta Bar Gidan Yari

Rudani Yayin Da Shahararriyar 'Yar Tiktok, Murja Kunya, Ta Bar Gidan Yari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

Jihar Kano - Ana cigaba da nuna damuwa kan rahotannin da ke cewa fitacciyar Tiktok, Murja Kunya, ta tsere daga gidan gyaran hali na Kano.

Daily Trust ta rahoto cewa kotun shari'ah da ke zamanta a Gama PRP na birnin Kano ta bada umurnin a tsare 'yar Tiktok din a gidan gyaran hali na Kurmawa.

An sako Murja Kunya daga gidan yarin Kano
Murja Kunya ta bar gidan gyaran hali na Kano. Hoto: Murja Kunya
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun a ranar Talata ne 'yan Hisbah na jihar Kano suka kama shahararriyar 'yar TikTok din bayan samun korafi daga makwaftanta kan zargin ayyukan badala.

Yayin da aka gurfanar da ita a kotu, an zarge ta da rashin da'a da yunkurin koya wa kananan 'yan mata karuwanci.

Kara karanta wannan

Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da shari'ar Murja Kunya

Daga bisani alkalin kotun ya bada umurnin a ajiye ta a gidan gyaran hali har zuwa ranar 21 ga watan Fabrairu.

Da ya ke magana kan lamarin, kakakin kotun, Muzammil Ado Ibrahim Fagge, ya ce ba su da masaniya kan lamarin.

Ya ce:

"Mun ji wai an sako ta daga gidan gyaran hali. Alkalin ya yanke hukunci kan ko zai bada belinta ko akasin haka a ranar 20 ga watan Fabrairu.
"Ba mu san abin da ya faru ba. Ba zai yi wu a canja abin da ya faru a kotu ba musamman kan yarinyar da ba wannan ne karon farko da aka kawo ta kotu ba. An taba kaita babban kotun shari'ah da ke Filin Hockey a kan irin wannan batun.
"Abin da muka sani shine Murja tana gidan gyaran hali amma ba zan yi mamaki ba idan an bada belinta."

Martanin Kakakin Gidan Gyaran Hali Kan Sakin Murja Kunya

Kara karanta wannan

Innalillahi: Ƴan bindiga sun kai kazamin hari kan matafiya, sun tafka mummunar ɓarna a jihar Arewa

Da ya ke martani kan lamarin, kakakin gidan gyaran hali na Kano, Musbahu Kofar Nassarawa ya ce an sake ta bayan kotu ta bada umurni.

Ya ce:

"Gidan gyaran hali na aiki ne da ka'idoji kamar banki, takarda da ya shigo da kai shine zai fita da kai. Idan akwai tsaiko, ba za a amince da shi ba.
"Muna da rattaba hannun dukkan alkalai a jihar. Dole alkali ya rattaba hannu a kawo ka haka kuma idan za a sake ka.
"A batun Murja, babu wanda ya tsere daga gidan gyaran hali. Idan ka yi yunkurin haura katanga, ana iya bindige ka kuma muna da jami'ai a kofofin daban-daban.
"Abin mamaki ne a ce ta tsere. Umurnin kotu ya kawo ta kuma umurin kotu ya fitar da Murja Kunya."

Martanin Hisbah na Kano kan sakin Murja Kunya

Jami'in Hisbah na Kano wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce sakin na Murja ba zai shafi ayyukan jami'ansu ba kuma ba za su yi a kasa a gwiwa ba domin yaki da ayyukan badala a jihar.

Kara karanta wannan

Kano: Kotun Shari'ar Musulunci ta yi hukunci kan 'yar Tiktok, Ramlat, ta fadi dalilai

Bayan Murja Kunya, Hisbah Ta Sake Kama Wata ‘Yar TikTok a Kano

Hukumar Hisbah ta jihar Kano, ta kama wata shahararriyar 'yar TikTok, Ramlat Princess, kan zargin wallafa wasu bayanai a shafinta na TikTok da ke tallata madigo.

Hukumar wacce aka kafa domin ta yi yaki da alfasha a Kano, ta tabbatar da kamun ta wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na TikTok.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164