Wahalar Rayuwa: 'Yan Sanda Sun Kama Mutane 2 Kan Satan Kebura a Legas
Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Jihar Legas - Rundunar 'yan sanda reshen Jihar Lagos ta kama wani Amisu Ahmed da Abdullahi Ubala bisa zargin satar wayar wuta a karamar hukumar Oshodi da ke Jihar.
Rundunar yan sandan ce ta sanar da hakan a shafinta na Tuwita (X) ranar Lahadi.
Sanarwar ta ce, jami'an yan sanda reshen ofishin Isolo ta cafke tare da kwace wayoyin wutar da aka sato a hannun wasu bata gari.
Ga abin da sanarwar ta ce:
"Jami'an yan sanda reshen ofishin Isolo, bayan samun korafi daga mazauna yankin, sun cafke wasu bata gari wanda ke da halayyar cire kayayyakin wuta a gine-ginen da ba a kammala ba tare kuma da kama wayoyin wuta da sauran kayan aikin da suke aikata laifin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Wanda ake zargin, Amisu Ahmed 'namiji' mai shekaru 27 da Abdullahi Ubalawa mai shekaru 26 za su fuskanci shari'a bayan kammala bincike."
A shekarar da ta gabata, Punch ta ruwaito cewa hukumar yan sandan Lagos tayi bajakolin barayin wayar wuta 8, tare da kwace fiye da mita 100 na wayar wuta daga wanda ake zargi.
Asali: Legit.ng