'Yar Najeriya Ta Saka Kowa Alfahari, Ta Zama Mafi Kwazo a Makarantar Kiwon Lafiya Ta Burtaniya

'Yar Najeriya Ta Saka Kowa Alfahari, Ta Zama Mafi Kwazo a Makarantar Kiwon Lafiya Ta Burtaniya

  • Wata ‘yar Najeriya ta sanya al’umma alfahari bayan nasarar kammala karatun digiri na biyu a fannin dokokin kiwon lafiya
  • An bayyana yadda ta fito a matsayin gagara-badau a wannan fanni a tsakanin turawa duk da ‘yar Najeriya ce
  • Rahoto ya ba da kadan daga tarihin aikinta da kuma irin gudunmawar da take son ba kasarta a nan kusa

Salisu Ibrahim ne babban editan (Copy Editor) sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Landan, Burtaniya - ‘Yar Najeriya Douye Nomayo ta sami lambar yabon wacce ta fi kowa kwazo a makarantar kiwon lafiya a Jami'ar Landan.

Likitar wacce ta kammala karatunta da sakamako mafi nagarta ta sami kyautar ne bayan ta sami digiri na biyu a fannin Dokokin Kiwon Lafiya daga Jami'ar London.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Gwamnonin PDP sun nemi Tinubu ya yi murabus, sun fadi dalili

Kafin ta hijira zuwa kasar Ingila ta Birtaniya, Nomayo ya yi aiki a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Yenagoa a jihar Bayelsa, na tsawon shekaru tara.

'Yar Najeriya ta sanya kowa alfahari a Landan
'Yar Najeriya ta sanya kowa alfahari a jami'ar Landan | Hoto: CityUniLondon
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin da yasa ta zabi fannin dokokin kiwon lafiya

Nomayo a tattaunawarta da manema labarai ta ce ta yanke shawarar yin karatun digiri na biyu a fannin dokokin kiwon lafiya ne saboda sha'awarta ga aikin gwamnati, The Nation ta ruwaito.

Da take bayani, ta ce:

“A lokacin da na yi aiki a asibiti, na ga mutanen da ke shan wahala wajen neman magani da kayan jinya, saboda tsada ko rashin samuwarsu.
"Na gane cewa dole ne ma'aikatan kiwon lafiya su kara shiga siyasa don samun warware matsaloli a fannin kiwon lafiya a kan tsarin siyasa cikin sauri.”

Meye alakar abin da ta karanta da Najeriya?

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya samu babban mukami, kungiyar AU ta ba shi nauyi a nahiyar Afrika

Da take karin haske game da abin da ta koya, jaridar Vanguard ta ruwaito ta tana cewa:

“Na fahimci harkokin kudi da siyasa na tsara dokoki a fanni kiwon lafiya kuma na koyi yadda ake tsarawa, kimantawa da inganta dokokin da ake da su.
"Kasashe da dama sun yi gyare-gyaren tsarin kiwon lafiya kuma za a iya amfani da kwarewarsu don samar da sauye-sauyen da suka dace alakar kudi da kuma aminci ga asibitoci da kuma al'ummar Najeriya.”

Da yake karin haske, Nomayo ya dora laifin hijirar kwararrun likitocin Najeriya zuwa kasashen ketare, musamman Birtaniya da Amurka kan rashin tsaro da lalacewar tattalin arzikin Najeriya.

Dan Najeriya mai tallan doya a Landan

A wani labarin, Legit ta samo bidiyon wani dan Najeriya da ya dage da yin tallan doya a birnin Landan.

A bidiyon, an ga mutumin a bakin titi dauke da hajarsa, lamarin da ya jawo cece-kuce da martanin jama’a.

An kuma gano cewa, matashin ya samu kudaden a matsayin karin abin hannu a wannan sana’ar da ya kama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.