Tsadar Rayuwa: Ku Kwantar da Hankulanku, Malamin Addini Ya Bai Wa ’Yan Kasa Tabbaci, Ya Fadi Dalili
- Fasto Mustapha Solomon ya yi magana kan halin da ake ciki a Najeriya inda ya ce komai zai daidaita a kwantar da hankula
- Faston ya roki ‘yan Najeriya da su kara hakuri ganin yadda kasar ta sauya gaba daya ta bangaren rashin tsaro da halin kunci
- Faston ya ce ya na da tabbacin cewa dukkan kalubalen kasar za su wuce kuma za ta fita daga wannan kangi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Fitaccen Malamin addini ya kara rokon ‘yan Najeriya da su kara hakuri komai zai dawo yadda ya kamata a kasar.
Shugaban cocin Seed of Christ Golden, Fasto Solomon Mustapha shi ya bayyana haka inda ya ce matsalolin kasar masu gushewa ne.
Mene Faston ke cewa kan halin kunci?
Faston ya ce ya na da tabbacin cewa dukkan kalubalen kasar za su wuce kuma za ta fita daga wannan kangi, cewar The Nation
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mustapha ya ce hasashen da ya yi cewa naira za ta tashi tare da karya darajar dala zai faru inda ya ce abin da ubangiji ya fada masa kenan.
Ya gargadi gwamnati da kuma ‘yan Najeriya da su cire ran cewa malaman addin ne za su cire kasar a halin da take ciki.
Malamin ya bayyana haka ne yayin hira ta musamman da ‘yan jaridu kan halin da kasar ke ciki, cewar Vanguard.
Rokon da ya tura ga 'yan Najeriya
A cewarsa:
“Aikin malami shi ne sanar da abin da ubangiji ya fada masa, lokacin da na ce dala za ta fadi kawai ina bin umarnin ubangiji ne.
“Kuma hakan ya faru inda naira ta kara daraja, amma daga baya darajar ta fara zubewa, mutane su na ba ni mamaki, malami aikinsa hasashe ne ba wai daga darajar naira ba.
“Hasashe kan Najeriya shi ne kasar za ta dawo kan turba, kuma dole mu sani hasashen malamai ba dole ya faru a lokaci daya ba.”
Sultan ya yi magana kan halin kunci
Kun ji cewa Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar ya gargadi hukumomi kan daukar mataki a halin da ake ciki yanzu.
Sultan ya ce a yanzu an kure ‘yan Najeriya musamman matasa kuma an kai su bango komai zai iya faruwa idan ba a dauki mataki ba.
Asali: Legit.ng