Tsadar Rayuwa: Jigon PDP Ya Bayyana Wanda Za a Dorawa Alhakin Yunwa da Wahalar da Ake Ciki a Kasa

Tsadar Rayuwa: Jigon PDP Ya Bayyana Wanda Za a Dorawa Alhakin Yunwa da Wahalar da Ake Ciki a Kasa

  • An ɗora alhakin halin taɓarɓarewar tattalin arziƙin da jam'iyyar APC ta jawo a ƙasa a kan ƴan Najeriya
  • Wani jigon jam’iyyar PDP Dr Segun Showunmi ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa ta musamman da Legit.ng ta yi da shi
  • Ya bayyana cewa jam’iyyar APC ba ta da hurumin komawa mulki bayan shafe shekaru takwas tana ganawa ƴan Najeriya wahala

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Dr Segun Showunmi, tsohon ɗan takarar gwamna a jam'iyyar PDP a jihar Ogun, ya tabbatar da cewa nauyin ƙalubalen tattalin arzikin da ƙasar nan ke fuskanta yana kan ƴan Najeriya.

Dr Segun Showunmi, a yanzu yana neman kujerar shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa.

Kara karanta wannan

Babban nasara: Dakarun sojoji sun samu gagarumar nasara kan 'yan ta'adda, sun halaka da dama

Showunmi ya magantu kan halin da ake ciki a kasa
Showunmi ya ce Tinubu na cikin mawuyacin hali Hoto: Segun Showunmi, Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Showunmi ya jaddada cewa, duk da cewa ƴan Najeriya suna sane da wahalhalu da wuyar da gwamnatin da ta shuɗe a ƙarƙashin jam’iyyar APC ta tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta jawo, amma sun zaɓi su ƙara zaɓenta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata hira ta musamman da Legit.ng ta yi da jigon na PDP ya ce:

“Na ɗora alhakin ƙalubalen ƙasar nan kan ƴan Najeriya, Meyasa? Saboda ƴan Najeriya suna da gwamnatin APC da ta ƙare a 2023, sun san yadda abubuwa suke tafiya. Suna kuma sane da ɗumbin ƙalubalen da take fuskanta a lokacin.
"Saboda haka, ƴan Najeriya ba su da damar dawo da APC. Saboda ta hanyar dawo da su, ya zama da wahala ga mutanen da ke kan mulki a yanzu su bincikesu yadda ya dace."

Tinubu ya shiga cikin mawuyacin hali

Ya bayyana cewa halin da Tinubu yake ciki mawuyaci ne domin ya gaji durƙusashshen tattalin arziƙi daga abokansa da magabacinsa.

Kara karanta wannan

Ba a gama da batun Emefiele ba an bankado wata sabuwar badakala a CBN, bayanai sun fito

Dr Showunmi ya ce Shugaba Tinubu ya ya shiga ƙaƙaniƙayi kuma yana ƙoƙarin kada ya ɓata ran manya ƴan jam'iyyarsa, kuma yana son ya ƙyalesu wanda hakan zai cutar da ƴan Najeriya.

Ya yi nuni da cewa abubuwa irin waɗannan suke sanya wa a kasa binciken gwamnati yadda ya dace ba tare da nuna bambanci da son kai ba.

Afenifere Ta Goyi Bayan Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiƴar Yarabawa ta Afenifere ta ccacaki masu sukar gwamnatin Tinubu kan halin matsin da ake ciki a ƙasa.

Ƙungiyar ta bayyana cewa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya kamata a ɗorawa alhakin wahalar da ake sha yanzu a ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng