“Da Tallafi, Babu Wuta”: Shehu Sani Ya Magantu Kan Shirin Tinubu Na Janye Tallafin Wutar Lantarki

“Da Tallafi, Babu Wuta”: Shehu Sani Ya Magantu Kan Shirin Tinubu Na Janye Tallafin Wutar Lantarki

  • Jama'a na ci gaba da cece-kuce kan shirin da gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu ke yi na janye tallafin wutar lantarki
  • Sanata Shehu Sani ya yi al'ajabin abin da 'yan Najeriya za su amfana da shi, saboda da cikakken tallafin, babu tsayayyiyar wutar lantarki
  • Tsohon 'dan majalisar ya dasa ayar tambaya kan yunkurin gwamnatin tarayya yayin da 'yan Najeriya suka gabatar da sauran zabuka idan gwamnati ta yanke shawarar gwanjon sa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Tsohon sanatan Kaduna Shehu Sani ya nuna damuwa yayin da gwamnatin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta sanar da shirinta na janye tallafin wutar lantarki domin amfani da wuta yadda ya kamata a kasar.

Tsohon 'dan majalisar ya yi mamakin halin da 'yan kasar za su shiga bayan sanarwar da gwamnatin ta yi, yayin da ya bayyana cewa "da tallafin lantarki ma, babu wuta."

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tinubu ya ki karbar shawarar bude iyakoki da kayyade farashin abinci

Shehu Sani ya nuna damuwa kan shirin cire tallafin lantarki
“Da Tallafi, Babu Wuta”: Shehu Sani Ya Magantu Kan Shirin Tinubu Na Janye Tallafin Wutar Lantarki Hoto: Shehu Sani (Senator Shehu Sani), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Sani ya yi hasashen nan ne a wata wallafa da ya yi a shafinsa na X a ranar Jumaá, 16 ga watan Fabrairun 2024, kuma 'yan Najeriya sun yi martani daban-daban.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ku tuna cewa gwamnatin tarayya a ranar Laraba, 14 ga watan Fabrairy, ta ayyana cewa yanzu "zai yi wahala ta ci gaba da biyan tallafin wutar lantarki".

Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce Najeriya ba za ta iya ci gaba da bayar da tallafin wutar lantarki ba, inda ya ce kasar na bukatar fara aiwatar da tsari na daban mai inganci.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan Najeriya a fadin kasar ke fuskantar matsalar rashin wuta sakamakon faduwar da babban layin wuta a 2023, tare da tsadar man fetur.

Yayin da ake tsaka da fama da matsalolin tattalin arziki a Najeriya, tsohon dan majalisar kuma jigon jam'iyyar PDP ya rubuta:

Kara karanta wannan

"Sun rasa muryarsu karkashin Buhari": Shehu Sani ya magantu yayin da sarakunan Arewa ke sukar Tinubu

"Da tallafin wutar lantarki, babu wuta...me zai faru idan aka cire tallafin?

Jama'a sun yi martani

@AGINAS ya rubuta:

"Bayar da tallafin wutar lantarki ba zai kawo kowani banbanci ba."

@JVeebrand ya yi martani:

"'Yan Najeriya za su roki wuta daga lahira kamar yadda Adeboye ya ce.

@Northernman00 ya rubuta:

"Z a fi samun wuta, ka yarda da tsarin Shehu Sani! Ka daina neman aibun labarin, ka tunga kyautata zato a kodayaushe don Allah."

Majalisa ta bukaci sanya tallafi wajen maniyyata

A wani labarin, mun ji cewa majalisar Wakilan Najeriya ta bukaci saka tallafi a harkar jigilar maniyyata aikin hajji saboda muhimmancinsa.

Majalisar ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta saka tallafi a hajjin bana don bai wa maniyyata damar zuwa kasa mai tsarki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng