Daga Karshe An Bude Babban Kantin Abuja da Aka Rufe, An Fadi Laifi 1 da Suka Aikata
- Hukumar FCCPC ta sanar da bude babban kantin siyayya na Sahad da ta rufe a yankin Garki da ke Abuja a ranar Juma'a
- Hukumar mai kare hakkin masu amfani da kayayyaki ta kasa ta ce an rufe kantin ne saboda kama su da laifin saka farashin kaya ba yadda suke a zahiri ba
- An rahoto cewa kantin na saka farashi mai sauki a jikin wajen zuba kaya sannan su caji kwastamomi fiye da haka yayin biyan kudi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura
Abuja - Hukumar kula da kare hakkin masu amfani da kayayyaki ta kasa (FCCPC) ta ce ta bude babban kantin siyayya na Sahad da ke yankin Garki, a babban birnin tarayya Abuja, jaridar The Cable ta ruwaito.
Tsadar kaya: Tsohon hadimin Buhari ya magantu yayin da gwamnatin Tinubu ta rufe babban kanti a Abuja
A ranar Juma'a, 16 ga watan Fabrairu ne jami'an hukumar ta FCCPC suka rufe babban kantin saboda samunsu da laifin "yaudara wajen saka farashi da kin bayyana gaskiya a farashin kayansu".
Wani laifi kantin Sahad ya aikata?
Hukumar ta FCCPC ta ce bincike ya nuna cewa kantin Sahad na saka farashi mai sauki a jikin wajen zuba kaya sannan su caji kudi da yawa a wajen biyan kudi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar ta ce an gudanar da binciken ne a dukkanin kantunan Sahad da ke Abujja, a kokarin da ake na ganin an fahimci lamarin da kyau, tare da daukar matakin gyara a fadin wurin.
FCCPC ta ce ta gayyaci mambobin kwamitin gudanarwa na kantin domin su kare kansu, amma suka ki amsa gayyatar.
An bude kantin Sahad bayan fahimtar juna, FCCPC
Adamu Ahmed Abdullahi, mukaddashin mataimakin hukumar ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa bayan fahimtar juna da jajircewa daga kantin Sahad na bayyana gaskiya a farashin kaya, an bude kantin.
Abdullahi ya ce hukumar FCCPC ta bude kantin a ranar 16 ga watan Fabrairu da misalin karfe 7:00 na yamma, rahoton Punch.
Ya kuma ce ana bukatar 'yan kasuwa su dunga baje farashin gaskiya domin kwastamomi su san ainahin farashin abin da suke siya tare da yanke hukunci kan ko su siya, musamman a wannan lokaci da ake ciki.
Kudi ya yi layar zana a kantin Sahad
A wani labari na daban, katafaren shagon nan na sayar da sayar da kaya a jihar Kano Sahad Store, dake kan babban titin zuwa Gidan Zoo ya kori ma'aikata sama da mutane saba'in saboda rashin ciniki da yake fuskanta.
Sannan kuma shagun ya bayyana yadda makudan kudade da yawansu ya kai kimanin naira miliyan dari biyu (N200m) suka bace sama ko kasa har yanzu babu amo ba labari.
Asali: Legit.ng