Wata sabuwa: Haka kawai an wayi gari miliyan 200 tayi batan dabo a shagon Sahad Store na Kano
- An wayi gari katafaren shagon Sahad Store dake Kano ya kori ma'aikata sama da mutane saba'in
- Hakan ya biyo bayan rashin ciniki da kuma batan wasu makudan kudade da yawansu ya kai kimanin naira miliyan dari biyu a shagon
- Shugaban rukunan shagunan Alhaji Mijinyawa ya bayyana cewa ya san kaddarace ta fado masa kuma ya rungumeta, saboda haka yana so suma wadanda suka rasa aikinsu su rungumi kaddara
Wasu rahotanni sun nuna cewa katafaren shagon nan na sayar da sayar da kaya a jihar Kano Sahad Store, dake kan babban titin zuwa Gidan Zoo ya kori ma'aikata sama da mutane saba'in saboda rashin ciniki da yake fuskanta.
Sannan kuma shagun ya bayyana yadda makudan kudade da yawansu ya kai kimanin naira miliyan dari biyu (N200m) suka bace sama ko kasa har yanzu babu amo ba labari.
Wannan batan kudi shine ya sanya shugabanni masu gudanarwa na shagon suka dauki wannan mataki na korar ma'aikatan nasu guda saba'in da biyar.
KU KARANTA: A karon farko jam'iyyar PDP ta roki shugaba Buhari wata alfarma
Da manema labarai suka yi hira da shugaban rukunin wannan shaguna Alhaji Mijinyawa ya bayyana cewa matakin da ya dauka ba wai ya dauka kai tsaye bane, sai da ya hada da manajan shagunan, sannan ya kawo wani sabon manaja wanda zai cigaba da aiki a wajen.
Ya kuma kara da cewa kaddara ce ta same shi shine yasa wannan lamari ya faru, kuma shi ya riga ya dauki kaddara, saboda haka suma sauran ma'aikatan da aka kora a aiki suma su rungimi kaddara akan abinda ya same su.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng