Tsadar Abinci: Gwamnati Ta Rufe Wani Babban Kanti a Abuja, an Samu Cikakken Bayani
- Gwamnati ta rufe wani babban kantin Sahad da ke Garki, babban birnin tarayya, Abuja, bayan kama su da laifin cutar kwastomomi
- Hukumar kula da kare hakkin masu amfani da kayayyaki ta kasa (FCCPC) ce ta rufe kantin bayan da kantin ya karya dokar sashe na 115 (3)
- Rahotanni sun bayyana cewa ana zargin kantin Sahad da cajar kwastomomi kudin da suka haura wanda aka rubuta a jikin kayayyakin su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
FCT, Abuja - Kasa da awanni 24 bayan da shugaban kasa Bola Tinubu ya ba jami'an tsaro umarnin kamasu masu boye kayan abinci, hukumar FCCPC ta fara aiki.
Hukumar wacce ke kula da kare hakkin masu amfani da kayayyaki ta tarayya, ta rufe babban kantin Sahad da ke Garki, a babban birnin tarayyar, Daily Trust ta ruwaito.
An zargi shugabannin kantin da yin almundahana ta hanyar cajar kwastomomi kudin da suka haura wanda aka lika a jikin kaya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mukaddashin mataimakin shugaban hukumar FCCPC, Adamu Ahmed Abdullahi ne ya jagoranci sumamen.
Dokar da kantin Sahad ya karya - Abdullahi
Da yake zantawa da manema labarai, Abdullahi ya ce binciken farko da hukumar ta gudanar ya tabbatar da cewa masu gudanar da kantin suna ha'intar abokan ciniki.
Jaridar Leadership ta ruwato Abdullahi ya ce kantin zai ci gaba da kasancewa a rufe har sai an kammala bincike.
“Mun gano cewa akwai rashin gaskiya a farashin kayan kantin, wanda ya saba wa sashe na 115 (3) na dokar da ta ce ba a yarda kwastoma ya biya kudin kaya alhalin kudin ya haura wanda aka nuna masa.
“Sashi na 155 ya bayyana cewa duk wani kamfani da ya sabawa dokar za a ci tarar naira miliyan 100 haka kuma daraktocin kamfanin za su biya naira miliyan 10 ko kuma daurin watanni shida ko kuma duka biyun."
- A cewar Abdullahi.
Abdullahi ya yi nuni da cewa hukumar ta gayyaci shugabannin kantin domin su kare kansu kan zargin amma suka ki amsa gayyatar.
Gwamnati ta sa a kama masu boye kayan abinci
Hakan dai na zuwa ne bayan da gwamnatin tarayya da na jihohi suka hada kai don samar da kwamitin da zai magance matsalar boye kayan abinci a kasar.
Ministan watsa labarai, Mohammed Idris, ya bayyana hakan jim kaɗan bayan taron Shugaba Tinubu da gwamnoni da wasu shugabannin tsaro da ministoci a fadarsa da ke Abuja.
Da ya ke zantawa da manema labarai, ministan ya zargi 'yan kasuwa da boye kayan abinci, inda ya ce an ba jami'an tsaro izinin kama duk wanda aka kama da aikata wannan laifi.
Asali: Legit.ng