Gwamnan Arewa Ya Fadi Dalili 1 da Ya Sa Tubabbun Mayakan Boko Haram Ba Za Su Koma Kashe-Kashe Ba
- Gwamnatin jihar Borno ta yi magana kan dalilin da ya sa tubabbun ƴan ta'addan Boko Haram ba za su iya komawa ga kashe-kashen da suke yi a baya ba
- Gwamnatin jihar ta Arewa maso Gabas ta ce ƴan Boko Haram da suka tuba tuni sun rantse da Al-Qur’ani mai girma cewa sun zama ƴan Najeriya nagari
- A cewar gwamnati, duk wani tubabben ɗan Boko Haram da ya koma daji domin yakar al’ummar Najeriya, bai yi wa kansa daidai ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Maiduguri, jihar Borno - Gwamnatin jihar Borno ƙarƙashin jagorancin Gwamna Babagana Zulum, ta ce tubabbun mayaƙan Boko Haram ba za su iya komawa yin kashe-kashe ba.
Gwamnatin jihar ta Arewa maso Gabashin Najeriya ta ce tubabbun mayaƙan ba za su iya komawa ga mummunanr ɗabi'arsu ba, domin sun riga sun rantse da Al-Qur’ani mai tsarki, cewar rahoton The Punch.
Tubabbun ƴan ta'adda za su cika alƙawari
Hajiya Zuwaira Gambo, kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban al’umma ta jihar Borno, ta musanta cewa ƙaruwar ayyukan ta'addanci a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, saboda wasu tsoffin ƴan ta’addan Boko Haram sun koma ruwa ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami'ar gwamnatin ta Borno tayi magana a ranar Laraba, 14 ga watan Fabrairu, a wurin wani taron jama’a, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
A kalamanta:
"Ba gaskiya bane cewa tubabbun mayaƙan Boko Haram suna komawa daji suna ci gaba da fafatawa. A cikin sama da 160,000 da suka tuba, mun riga mun mayar da sama da 70,000 a yankunansu."
Ta ƙara da cewa:
"Mun sanya kowannensu ya yi rantsuwar da ta dace da Al-Qur’ani mai girma cewa ba zai taɓa komawa daji yaƙi ba."
Bam Ya Halaka Mutane a Borno
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani bam da ƴan ta'addan Boko Haram suka sanya, ya salwantar da ran wasu matafiya a jihar Borno.
Mutanen nan dai waɗanda masu sana'ar yin itace ne, motarsu ta taka bam ɗin ne lokacin da suke kan hanyar wajen garin ƙauyen Pulka.
Asali: Legit.ng