Shugaba Tinubu Zai Gana da Gwamnonin Najeriya Kan Wani Muhimmin Abu, Bayanai Sun Fito
- Shugaba Bola Tinubu zai gana da ɗaukacin gwamnonin ƙasar nan 36 kafin ya haɗu da takwarorinsa na nahiyar Afirika domin halartar taron AU
- Ganawar da Tinubu zai yi da gwamnonin za ta kasance ita ce ta biyu tun bayan da ya hau kan karagar mulkin Najeriya
- Ku tuna cewa a kwanakin baya gwamnonin PDP sun soki manufofin tattalin arziƙin Tinubu amma fadar shugaban ƙasa ta caccaki gwamnonin na PDP
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Rahotanni sun bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya gayyaci gwamnoni 36 a Najeriya domin yin wani muhimmin taro a fadar shugaban ƙasa da safiyar ranar Alhamis, 15 ga watan Fabrairu.
Taron zai gudana ne kafin Shugaba Tinubu ya wuce ƙasar Habasha domin halartar taron ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU).
Taron dai zai kasance irinsa na biyu tun bayan da Tinubu ya hau kan karagar mulki a ranar 29 ga watan Mayu, kuma za a yi shi ne kan matsalar ƙalubalen tattalin arziƙi da rashin tsaro a ƙasar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An bayyana hakan ne a wani sako da jaridar AriseTV ta wallafa a shafinta na Twitter da safiyar ranar Alhamis, 15 ga watan Fabrairun 2023.
Taron dai na zuwa ne bayan gwamnonin PDP sun fito sun soki manufofin Shugaba Tinubu kan tattalin arziƙi, da kuma yadda rayuwa ta yi a ƙasar nan.
Me yasa gwamnonin PDP suka caccaki Tinubu
Gwamnonin na PDP sun yi tsokaci game da hauhawar farashin kayayyaki, ƙaruwar yunwa, aikata laifuka, da kuma yawan mace-macen da ake fama da su a ƙasar nan.
Sai dai fadar shugaban ƙasa ta mayar da martani kan wannan tsokaci inda ta soki gwamnonin kan yadda suke gudanar da ayyukansu, musamman ganin yadda suka kasa biyan albashi duk da ƙarin kason da gwamnatin tarayya ke ba su.
Zanga-zanga dai ta ɓarke a wasu jihohi saboda tsadar rayuwa, inda ƴan Najeriya ke neman a magance matsalar tattalin arziƙi.
A sakamakon hakan, Shugaba Tinubu ya ba da umarnin a gaggauta sakin sama da tan 100,000 na kayan abinci iri-iri daga rumbunan ajiya na ƙasa da kuma ƙungiyar masu casa ta Najeriya.
Sarakunan Arewa Sun Aike da Saƙo Ga Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa sarakunan gargajiya na yankin Arewacin Najeriya sun aike da saƙo ga shugaban ƙasa Bola Tinubu.
Sarakunan sun koka cewa ba su san yadda za su lallashi mutanensu ba, inda suka buƙaci shugaban ƙasan da ya tashi tsaye ya nemo mafita kan halin da ake ciki a ƙasa.
Asali: Legit.ng