Tsadar Rayuwa: Sarkin Musulmi Ya Fadi Masifar da Za Ta Faru Idan Ba a Dauki Mataki Ba, Akwai Dalilai

Tsadar Rayuwa: Sarkin Musulmi Ya Fadi Masifar da Za Ta Faru Idan Ba a Dauki Mataki Ba, Akwai Dalilai

  • Sarkin Musulmi ya gargadi hukumomi kan matsifar da take tunkaro Najeriya idan har ba a dauki mataki ba
  • Sultan Sa’ad Abubakar ya ce a yanzu mutanen Najeriya sun fusata lokaci kawai suke jira don yin daukar mataki
  • Sultan wanda shi ne shugaban sarakunan gargajiya a Arewacin Najeriya ya ce rashin aikin yi da yunwa matsala ce babba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar ya nuna damuwa kan yadda aka bar matasa babu aikin yi.

Sultan wanda shi ne shugaban sarakunan gargajiya a Arewacin Najeriya ya ce rashin aikin yi da yunwa ba karamar matsala ba ce.

Sarkin Musulmi ya hango barazana kan halin da ake ciki
Sarkin Musulmi ya yi gargadi ga hukumomi kan tsadar rayuwa. Hoto: Sultan Sa'ad Abubakar.
Asali: Twitter

Mene Sarkin Musulmi ke cewa?

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Sanatan Kano ya yi magana kan matakan da Tinubu ke dauka, ya yi alkawari a bangarensa

Sarkin ya ce wannan yanayi da ake ciki kawai lokaci ne bai yi ba don Najeriya na dane ne a kan bam ko wane lokaci za ta tarwatse, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai Alfarmar ya bayyana haka ne a yau Laraba 14 ga watan Faburairu a Kaduna yayin taron sarakunan gargajiya a Arewa.

Ya ce a yanzu an iso wata gaba wacce idan ba a dauki mataki ba komai na iya faruwa a ko wane lokaci.

Ya kara da cewa ‘yan Najeriya sun gama fusata kuma an kai su bango wanda dole a dauki mataki ko kuma abin da ba a so ya faru, cewar Vanguard.

Shawarin da ya bayar ga hukumomi

A cewarsa:

“Mun yi zama sau da yawa kan tsaro, talauci da rashin tsaro ba abu ba ne da zamu nade hannayenmu muna kallo, na sha fada akwai matsala a Najeriya musamman a Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

AFCON: Ana saura kwana 4 aurensa ya rasu, cewar iyalan marigayi Ayuba a Kwara, bayanai sun fito

“Bai kamata mu dauka da wasa ba, mutane sun yi shiru saboda muna fada musu cewa komai zai daidaita, ina tsoron ranar da za su ce ba za su sake sauraranmu ba.
“Mun iso wata gaba wacce dole a dauki mataki saboda mutane sun gama fusata, amma duk da haka sun yarda akwai masu yi musu magana su ji.”

Sultan ya ce dole a samar wa matasa aikin yi saboda kamar yadda ya sha fada Najeriya na zaune ne kan bam ko wane lokaci za ta iya fashewa.

PDP ta shirya yin adawa mai amfani

A baya, kun ji cewa jam’iyyar PDP a Najeriya ta shirya yin adawa mai ma’ana ganin yadda komai ya tabarbare.

Jam’iyyar ta ce ba za ta zuba ido ba ta na ganin yunwa da rashin tsaro zai gurgunta Najeriya ta yi shiru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.