Dubu Ta Cika: An Kama Hatsabiban Ƴan Bindiga 7 da Ake Nema Ruwa a Jallo Tare da Kwato N9m
- Dakarun ƴan sanda sun cafke riƙaƙkun masu garkuwa da mutane da ake nema ruwa a jallo a birnin tarayya Abuja
- Kwamishinan ƴan sandan Abuja, CP Benneth Igweh, ya bayyana cewa jami'ai sun kuma kwato kuɗin fansa N9m daga hannun masu garkuwan
- Ya ce tuni waɗanda suka shiga hannun suka amsa laifukan su kuma suna bada bayanai masu amfani domin kama sauran ƴan tawagarsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Jami’an rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya sun kama wasu mashahuran masu garkuwa da mutane bakwai a Abuja.
Bayan kama hatsabiban ƴan bindigan waɗanda suka shahara a garkuwa da mutane, dakarun ƴan sandan sun kwato N9m na kuɗin fansa daga hannunsu.
Wike ya sanya babbar kyauta don cafko wasu rikakkun masu garkuwa da mutane a Abuja, bayanai sun fito
Kwamishinan ƴan sandan FCT Abuja, CP Benneth Igweh, ne ya bayyana haka yayin nuna waɗanda ake zargin ranar Laraba, 14 ga watan Fabrairu, Daily Trust ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
CP ya ce dakarun ofishin yan sanda na Utako ƙarƙashin jagorancin CSP Victor Godfrey, a wani samamen haɗin guiwa da suka kai Tudun Wada Lugbe da Pyakasa suka kama waɗanda ake zargin.
Su waye hatsabiban masu garkuwan da aka kama a Abuja?
Ya kuma faɗi sunayen ƙasurguman masu garkuwan da aka kama da suka haɗa da Usman Muazu daga Kwali a FCT, Aliyu Mohammed ɗan asalin Pumpomare a Borno da Awwal Dahiru wanda ya fito daga Gwagwalada.
Sauran sune, Rabi Sani, ƴar garin Safana a jihar Katsina, Madina Abubakar daga garin Guru, ƙaramar hukumar Lapai a Neja da Elimelech wanda ya fito daga Kauru a Kaduna.
Ragowar sun ƙunshi Saminu Idris daga garin Kauru a jihar Kaduna da kuma Mariji Iliya daga ƙaramar hukumar Mangu a jihar Filato.
A ina suke yawan aikata barna?
A cewarsa, wadanda ake zargin suna da alaka da manyan laifukan garkuwa da mutane a babban birnin tarayya Abuja da kewaye.
Kwamishinan ƴan sandan ya ƙara da cewa tuni dukkan waɗanda ake zargin suka amsa laifinsu kuma suna bada haɗin kai domin cafke sauran ƴan tawagarsu.
Ya ce sauran abubuwan da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da wukake, adduna, rigar kariya daga harsashi da kuma layu, Channels tv ta ruwaito.
EFCC ta kai samame jami'ar FUTA
A wani rahoton kuma Jami'an hukumar EFCC sun kai samame ɗakunan kwanan ɗaliban jami'ar fasaha ta tarayya (FUTA) da ke Akure, babban birnin jihar
Bidiyoyin da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna yadda jami'an suka kutsa cikin ɗakunan ta tsiya, an ce sun kama ɗalibai masu yawa.
Asali: Legit.ng