Tsohon SGF Ya Bayyana Yadda Aka Wawure $6.2m da Sa Hannun Buhari a CBN

Tsohon SGF Ya Bayyana Yadda Aka Wawure $6.2m da Sa Hannun Buhari a CBN

  • Tsohon sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Boss Mustapha, ya bayyana a gaban kotu domin bayar da shaida kan Emefiele
  • Boss Mustapha ya bayyana cewa da sa hannun tsohon shugaban Muhammadu Buhari na jabu aka fitar da $6.2m daga asusun CBN
  • Ya bayyana cewa bai san komai ba dangane da fitar kuɗin kuma ba Shugaba Buhari ba ne ya amince a fitar da kuɗin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Boss Mustapha, tsohon sakataren gwamnatin tarayya (SGF), ya bayyana a gaban babban kotun tarayya da ke Abuja, a ranar Talata, 13 ga watan Fabrairu.

Kamar yadda jaridar Tvc news ta ruwaito, Mustapha ya bayyana a matsayin shaida na masu gabatar da ƙara don bayar da shaida kan zarginsa da hannu a badaƙalar $6.2m da ake zargin tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.

Kara karanta wannan

Ma’aikacin CBN Ya Fadawa Kotu Yadda Emefiele Ya Cire $6.23m Lokacin Zaben 2023

Boss Mustapha ya ba da shaida a kotu
Boss Mustapha ya ba da shaida kan Emefiele a kotu Hoto: Boss Mustapha
Asali: Twitter

Boss Mustapha ya ce waɗanda suka cire $6,230,000 daga CBN ne suka yi sa hannun bogi na tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, a ranar 8 ga watan Fabrairun 2023, cewar rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da sa hannun jabu aka cire $6.2m daga CBN' - Mustapha

Tsohon SGF ɗin ya ce sa shi ma an yi sa hannunsa na jabu, inda ya ƙara da cewa bai san komai ba game da kuɗaɗen da aka fitar domin biyan ƴan ƙasashen waje masu sa ido kan zaɓe.

Kamar yadda shafin jaridar The Cable ya ruwaito, Mustapha ya ce bai san komai ba game da fitar da kuɗin har sai da ya bar ofis.

Ya kuma bayyana cewa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari bai amince da fitar da $6.2m don biyan masu sa ido kan zaɓen ba.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu zai lula zuwa kallon wasan ƙarshe na gasar cin kofin Afirka AFCON? Gaskiya ta bayyana

Mustapha ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya ba ta da wata alaƙa da biyan ƴan ƙasashen waje masu sa ido kan zaɓe.

A yayin da ake yi masa tambayoyi, tsohon SGF ɗin ya ce batun biyan masu sa ido kan zaɓe, abu ne da ya shafi hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), ba gwamnatin tarayya ba.

Ma'aikaci CBN Ya Bada Shaida Kan Emefiele

A wani labarin kuma, kun ji cewa an kira Ogau Onyeka Michael, wanda babban ma’aikaci ne a bankin CBN, domin ya bada shaida a shari’ar Godwin Emefiele da EFCC.

Ogau Onyeka Michael bayan ya bayyana a gaban kotun, ya yi bayanin abin da ya sa aka biya masu lura da zabe kudi $6,230,000 a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng